Rashin tsaro: Masu fadi a ji ne basu ilimantar da talakawa, Amaechi

Rashin tsaro: Masu fadi a ji ne basu ilimantar da talakawa, Amaechi

- Ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi, ya ce masu fadi a ji na kasar nan ne suka janyo matsalar tsaro

- Kamar yadda yace, 'ya'yan talakawan da masu fadi a ji a siyasa suka ki ilimantarwa ne suka rungumi ta'addanci

- Makusancin shugaban kasan yace talaucin da kasar nan ta shiga ya samo asali ne daga farkon mulkin farar hula

Rotimi Amaechi, ministan sufuri, ya dora laifin rashin tsaron Najeriya a kan masu fadi a ji a kasar nan, Jaridar The Cable ta wallafa.

Ya sanar da hakan ne yayin jawabin yayen dalibai karo na 34 na jami'ar Kalaba. Amaechi yasa masu fadi a ji a harkar siyasar Najeriya sun yi watsi da talakawa wanda hakan yasa talakawan suka fada miyagun laifuka.

"Ba zai yuwu a ce mun kasa gane abinda masu fadi a ji a kasar nan suka samar ba a fannin tsaron kasar nan ba. A wasu sassan kasar nan, masu fadi a ji a fannin siyasa sun kasa sauke nauyin dake kansu na ilimantar da 'ya'yan talakawa.

"Wadannan yaran da aka hana wasu hakkokinsu ne suka girma basu da wani zabi da ya wuce fadawa harkar ta'addanci," yace.

KU KARANTA: Muna matukar jin kunyar yadda ake sace dalibai a kasar nan, Fadar shugaban kasa

Rashin tsaro: Masu fadi a ji ne basu ilimantar da talakawa, Amaechi
Rashin tsaro: Masu fadi a ji ne basu ilimantar da talakawa, Amaechi. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa kwatas na ma'aikatan filin jirgi, sun sace matar aure

Minsitan ya kara da cewa, babu adalci a yadda ake alakanta talaucin kasar nan da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, saboda wannan halin da Najeriya ke ciki ya fara ne tun daga farkon mulkin farar hula.

"Domin gujewa tantama, bari in sanar da cewa tsabar talaucin da muke ciki a yau ya samu tushe ne tun kafin mulkin shugaban kasa Buhari.

"A takaice, wannan tsabar talaucin ya fara ne tun daga farko mulkin farar hula. Bai dace a dinga dora dukkan matsalar talaucin kasar nan a kan wani ko wannan mulkin ba," yace.

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa tana matukar jin kunyar yadda ake sace daliban makaranta a kasar nan.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a harkar yada labarai, Garba Shehu, ya sanar da hakan a ranar Juma'a.

Yace yadda ake yawan sace 'yan makaranta yana matukar baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kunya a gida Najeriya da ketare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel