Da Dumi-Duminsa: Buhari Ya Karbi Bakuncin Abdulsalami da Marwa a Aso Rock

Da Dumi-Duminsa: Buhari Ya Karbi Bakuncin Abdulsalami da Marwa a Aso Rock

- Tsohon shugaban mulkin soja, Abdulasalami Abubakar ya ziyarci shugaba Buhari a Aso Rock a ranar Juma'a 26 ga watan Maris

- Duk da cewa fadar shugaban kasa bata bayyana dalilin ziyarar ba, akwai yiwuwar tana da alaka da kallubalen tsaro a kasar

- A baya bayan nan, Abdulsalami ya bada wasu shawarwari kan yadda za a magance kallubalen tsaro a kasar

- Shugaban kasar ya kuma gana da shugaban hukumar yaki da miyagun kwayoyi, NDLEA, Mohammed Buba Marwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Juma'a ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar (mai murabus) a gidan gwamnati da ke birnin tarayya Abuja.

Mai taimakawa shugaban kasa na musamman a bangaren kafar watsa labarai, Bashir Ahmad ya sanar da hakan cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter @BashirAhmaad.

DUBA WANNAN: A Karo na Biyu, Masu Garkuwa Sun Sace Jigon APC a Lokacin Da Ya Tafi Duba Gonarsa

Da Dumi-Duminsa: Buhari Ya Karbi Bakuncin Abdulsalami da Marwa a Aso Rock
Da Dumi-Duminsa: Buhari Ya Karbi Bakuncin Abdulsalami da Marwa a Aso Rock. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Twitter

Har wa yau, a wani taron na daban, a ranar Juma'a, Shugaba Buhari ya gana da shugaban hukumar Yaki da Fatauci da Shan Miyagun Kwayoyi, NDLEA, Mohammed Buba Marwa a Aso Rock.

Duk da cewa hadimin shugaban kasar bai bayyana abinda za a tattauna yayin ganawar ba, Legit.ng na ganin akwai yiwuwar ziyarar na da alaka da kallabalen tsaro da ke adabar kasar.

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 9 a Ƙananan Hukumomin Giwa da Birnin Gwari a Kaduna

A baya-bayan nan, tsohon shugaban na mulkin soja, ya bada shawarwari kan yadda za a magance matsalolin tsaro da ake fama da su a Nigeria.

Daga cikin wasu abubuwan da ya zayyana, Janar Abdulsalami ya ce tattaunawa ko sulhu da yan bindigan ba shine abinda ya fi dacewa a yi ba.

A cewar Janar din mai murabus, hanyar da ta fi dacewa don warware matsalolin tsaro na yan bindiga da wasu kallubalen tsaron shine tabbatarwa ba a aikata laifin ba tunda farko.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Jami'an Hukumar Hisabah ta jihar Kano sun gargadi daliban Jami'ar Bayero da ke Kano wadanda ke zaune a gidajen da ke wajen makaranta su kauracewa aikata ayyukan masha'a, Vanguard ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan kama wasu dalibai mace da namiji a cikin daki guda a wani gida kwanan dalibai da ke kusa da kusa da jami'ar.

Jami'an na Hisbah sun kuma ce za a ci tarar N20,000 ga duk wani dalibi namiji da mace da aka kama su a daki guda kamar yadda majiyoyi suka shaidawa SaharaReporters

Asali: Legit.ng

Online view pixel