A Karo na Biyu, Masu Garkuwa Sun Sace Jigon APC a Lokacin Da Ya Tafi Duba Gonarsa
- Masu garkuwa da mutane sun sace jigon jam'iyyar APC, Mr Dominic Aqua Edem a jihar Cross Rivers
- An sace tsohon dan majalisar ne a ranar Alhamis yayin da ya tafi duba gonarsa a ranar Alhamis
- A shekarar 2015, masu garkuwa da mutane sun taba sace shi kuma sai da aka biya kudin fansa suka sako shi
Wasu da ke kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace wani jigon jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Cross River, Mr Dominic Aqua Edem, a yammacin ranar Alhamis karo na biyu.
Mr Edem, tsohon dan majalisar dokokin jihar Cross Rivers ne mai wakiltar mazabar Bakassi kuma mamba mai wakiltar Cross Rivers a Hukumar Cigaban Yankin Niger Delta, wato NDDC.
DUBA WANNAN: Kano: Hisbah za ta ci ɗaliban jami'a mace da namiji da aka kama a ɗaki ɗaya tarar N20,000 kowannensu
An ce shi ne a gonarsa yayin da ya tafi yin dubiyya.
"Eh, an sace shi a kauyensu na Ifang da ke Bakassi a lokacin da ya tafi duba gonarsa.
"Bayan ruwan sama da aka yi ranar Talata, ya tafi ya duba gonarsa a nan aka sace shi," kamar yadda hadiminsa, Mr Obun Ekanem ya shaidawa jaridar Vanguard.
Ya ce kawo yanzu masu garkuwan ba su tuntubi iyalansa ba.
KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 9 a Ƙananan Hukumomin Giwa da Birnin Gwari a Kaduna
An taba sace shi a 2015 lokacin da ya yi takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar Bakassi/Akpabuyo/Calabar South, an sako shi bayan biyan kudin fansa.
DSP Irene Ugbo, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Cross River bai daga wayarsa ba yayin da aka kira shi.
A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.
An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.
Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa jaridar Daily Trust kamun.
Asali: Legit.ng