Da duminsa: Gwamna Abiodun da Bankole sun shiga ganawar sirri

Da duminsa: Gwamna Abiodun da Bankole sun shiga ganawar sirri

- Honarabul Dimeji Bankole tare da Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun sun shiga ganawar sirri

- Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya, ya kaiwa Gwamna Abiodun ziyara har ofishinsa dake Abeokuta

- Tun karfe 4:25 na yamma suka shiga ganawar, wacce ba a san abinda suke tattaunawa ba har yanzu

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Dimeji Bankole, a ranar Alhamis ya shiga ganawar sirri da Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun a ofishinsa dake Oke-Mosan, Abeukuta, babban birnin jihar.

Bankole ya isa ofishin gwamnan wurin karfe 4:25 na yamma kuma ya samu tarba ta musamman daga gwamnan.

Premium times ta ruwaito cewa, su biyun sun shiga ganawar sirri wanda har a halin yanzu ba a san abinda suka tattauna ba.

KU KARANTA: Sojoji sun sheke 'yan bindiga 2 yayin da suka kai samame maboyarsu a Kaduna

Da duminsa: Gwamna Abiodun da Bankole sun shiga ganawar sirri
Da duminsa: Gwamna Abiodun da Bankole sun shiga ganawar sirri. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kyawawan hotunan sarakuna 3 masu karancin shekaru a Najeriya da cikakken tarihinsu

Tsohon kakakin majalisar tare da Gbenga Daniel, gwamnan jihar Ogun, sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karba bakuncinsu a fadarsa dake Abuja a ranar Litinin.

An nada Bankole a matsayin kakakin majalisar wakilai tsakanin 2007 zuwa 2011 karkashin jam'iyyar PDP kuma daga bisani ya yi takarar kujerar gwamnan jihar Ogun a karkashin jam'iyyar ADP.

Har zuwa karfe 6 na yammacin ranar Alhamis, Gwamna Abiodun da Bankole suna ganawar yayin da manema labarai ke wajen ofishin gwamnan suna jiransu.

A wani labari na daban, wata 'yar kasar Kenya, Nelius Wangui Mainawas ta gurfana a gaban wata kotu sakamakon zarginta da ake da sace wayoyi biyu daga wurin wani mutum da tace saurayinta ne.

An gurfanar da Maina a gaban wata kotun Makadara a ranar Talata, 23 ga watan Maris, a kan satar wayoyi biyu na Eric Basweti amma tace mai korafin saurayinta ne.

Ta yi korafin cewa ta sace wayoyin ne saboda ta rike su har sai ya biyata kudin motan da ya hana ta.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel