Buhari na daga cikin alheran da suka taba faruwa da Najeriya, Badaru

Buhari na daga cikin alheran da suka taba faruwa da Najeriya, Badaru

- Gwamna jihar Jigawa, Muhammad Badaru, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari na daga cikin alheran da suka taba faruwa a Najeriya

- Gwamnan ya sanar da hakan ne a shirin siyasarmu a yau inda ya bayyana nasarorin da aka samu a mulkin Buhari

- Badaru yace ba a lokacin Buhari aka fara fuskantar matsalar 'yan bindiga ba, saken shugabannin da suka gabata ne yasa ya gawurta

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya kwatanta shugaban kasa Muhammadu Buhari da abu mafi alheri da ya taba faruwa a Najeriya.

A yayin tattaunawa a shirin siyasarmu a yau wacce gidan talabijin na Channels yayi, gwamnan yace an samu manyan nasarori yayin mulkin.

Mai gabatarwa ya tambaya gwamnan ko ya sakankance da abinda takwaransa na APC yace, sai gwamnan yace: "Na yadda gaskiya, na amince dari bisa dari. Na san abinda na gada, na san matsalolin da na shiga. A wani lokaci na so tserewa. Amma da babu taimakon shugaban kasa Buhari, ba za mu daga kawunanmu a matsayin gwamnoni ba.

KU KARANTA: Bidiyon liyafar biki ana kwashe kudin liki da babban bokiti ya janyo cece-kuce

Buhari na daga cikin abubuwan alheri da suka taba faruwa da Najeriya, Badaru
Buhari na daga cikin abubuwan alheri da suka taba faruwa da Najeriya, Badaru. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ziyara na kai masa amma ya hana ni kudin mota, budurwar da ta sace wayoyin saurayi

"Idan za ku tuna, yayi belin duka jihohi, ya bamu tallafi ta yadda zamu biya albashin wata 18, ina nufin dukkan gwamnoni. Ya bamu tallafin aiwatar da ayyukan more rayuwa."

Gwamnan ya kara da cewa yadda shugaban kasa ke kokarin shawo kan matsalar makiyaya da manoma abun a jinjina masa ne.

"Rikicin makiyaya da manoma ya dade a kasar nan kuma ya tsananta ne a halin yanzu saboda shugabannin da suka shude basu mayar da hankali ba."

“Idan muka duba halin da ake ciki yanzu, satar jama'a da garkuwa dasu bai fara zamanin Buhari ba, ya dai cigaba ne," yace.

A wani labari na daban, dakarun rundunar Operation Thunder Strike da na Div 1 dake Kaduna sun ragargaza maboyar 'yan bindiga dake yankin Buruku a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba.

Kamar yadda kwamishinan ya sanar, wasu da ake zargin 'yan bindiga ne har mutum biyu sun sheka lahira yayin samamen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel