Bidiyon liyafar biki ana kwashe kudin liki da babban bokiti ya janyo cece-kuce

Bidiyon liyafar biki ana kwashe kudin liki da babban bokiti ya janyo cece-kuce

- Wasu ma'aurata sun bar kafar sada zumuntar zamani da maganganu bayan wani salo da suka dauka a yayin bikinsu

- A wani bidiyo da ya karade kafar sada zumunta, an ga wasu ango da amarya ana kwashe musu kudin liki a babban bokitin roba

- Wannan bidiyon ya karade kafar sada zumunta ya janyo cece-kuce saboda wasu sun ga gaskiyarsu yayin da wasu suka ga akasin haka

Wasu ma'aurata 'yan Najeriya da har yanzu ba a gane ko su waye ba sun karade kafar sada zumunta da salon da suka bayyana yayin bikinsu.

A wani bidiyo da @iam_steveola ya wallafa, an ga yadda ake ruwan kudi a wani biki da nairori amma ake kwashewa da wata katuwar bokitin roba.

Bidiyon ya nuna zukekiyar amaryar sanye da kayan gargajiya tana zaune yayin da take kallon wasu maza biyu suna kwashe kudin a bokitin roba.

KU KARANTA: Kyawawan hotunan sarakuna 3 masu karancin shekaru a Najeriya da cikakken tarihinsu

Bidiyon liyafar biki ana kwashe kudin liki da babban bokiti ya janyo cece-kuce
Bidiyon liyafar biki ana kwashe kudin liki da babban bokiti ya janyo cece-kuce. Hoto daga @iam_steveola
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zulum ya sake bankado 'yan gudun hijira na bogi a sansanin Maiduguri

Har yanzu dai ba a san lokaci ko wurin da aka yi bikin ba. Bidiyon tuni ya samu sama da tsokaci dubu takwas daga ma'abota amfani da Twitter.

Yayin da wasu ke mamakin yawan kudin da aka lika, wasu na nuna mamakinsu ne akan yadda ake kwashe kudin a bokitin roba.

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun halaka wasu mutum hudu da suka hada da ma'aikacin lafiya daya a kananan hukumomin Igabi da Jema'a na jihar Kaduna a ranar Litinin, sun bar wasu da raunika daga harsashi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, lamarin ya faru a kauyen Unguwan Lalle dake karamar hukumar Igabi da asibitin Niima dake kauyen Golgofa a karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna, jami'an gwamnatin jihar suka tabbatar.

A wata takarda da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar, ya sanar da cewa tun farko 'yan bindigan sun yi yunkurin rufe titin Kwanar Tsintsiya dake babbar hanyar Kaduna zuwan Abuja, amma sojoji suka fattatakesu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng