Kano: 'Yan Hisbah Sun Kai Samame Gidan Ɗaliban Jami'a, Sun Kama Mace da Namiji a Ɗaki Ɗaya

Kano: 'Yan Hisbah Sun Kai Samame Gidan Ɗaliban Jami'a, Sun Kama Mace da Namiji a Ɗaki Ɗaya

- Yan Hisbah a Kano sun kai sumame dakin kwanan daliban jami'ar BUK

- Sun yi nasarar kama wasu dalibai namji da mace da suke cikin daki guda

- Lamarin ya faru ne a unguwar Danbare da ke kusa da jami'ar BUK a Kano

Jami'an hukumar Hisbah a jihar Kano sun kai samame wasu dakunan daliban jami'ar Bayero da ke Kano inda suka kama dalibai mace da namiji a daki guda, Vanguard ta ruwaito.

SaharaReporters ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba a Danbare, wani gari da ke kallon kofar shiga jami'ar.

'Yan Hisbah Sun Kama Daliban Jami'a Mace Da Namiji a Daki Daya a Kano
'Yan Hisbah Sun Kama Daliban Jami'a Mace Da Namiji a Daki Daya a Kano. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi

An gano cewa yan hisban sun afka cikin dakunan daliban sun tafi da su ofishinsu.

Wata majiya ta ce sumamen da yan hisban suka kai ya tada hankulan wasu yan unguwar da suka kasa yin barci saboda tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo.

Hukumar ta Hisbah da aka kafa a wasu jihohin arewa domin tabbatar da bin dokokin addinin musulunci ta hana abubuwa kamar askin banza, sauke wando kasa da kugu, saka kida a wuraren biki da wasu abubuwan da suka saba koyarwar addinin musulunci.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Kaduna, Sun Kashe Huɗu Sun Raunta Wasu

A kwanakin baya, Hisbah ta aske wa wasu matasa kai sakamakon askin da suka yi na ado sun kuma kama wasu saboda saka wasu tufafi da suka ce ba su dace ba.

Sun kuma yi suna wurin kwace giya da lalata su a jihohin da suke aiki.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel