Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya roƙi FG tazo a yi taron sulhu da 'yan ta'adda

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya roƙi FG tazo a yi taron sulhu da 'yan ta'adda

- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya roƙi gwamnatin tarayya da tazo su haɗa kai su fuskanci matsalar tsaron jihar sa

- Gwamnan ya yi wannan kira ne ya yin da wakilan gwamnatin tarayya suka kai ziyara jihar don duba ɓarnar da gobara tayi a kasuwar Tudun-Wada, Gusau

- Yace indan da za'a tattauna da yan bindigar nan kamar yadda aka yi a baya da tsagerun Niger-Delta, da za'a iya kawo ƙarshen lamarin

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yi kira ga shugaban ƙasa mejo janar Muhammad Buhari ya amince a yi tattaunawar kawo zaman lafiya da yan ta'adda.

Gwamnan ya roƙi gwamnatin tarayya da su haɗa kai su shirya tsari mai kyau na kawo zaman lafiya ta hanyar tattaunawa da 'yan fashin don kawo karshen duk ta'addanci a faɗin jihar.

KARANTA ANAN: 'Yan Bindiga sun hallaka wani Sufeton 'yan sanda, Sun babbaka motarsu a Delta

Matawalle ya yi wannan kiran ne yayin da ya karɓi bakuncin wakilan gwamnatin tarayya, wanda alƙalin alƙalai na ƙasa (AGF) kuma ministan shari'a Abubakar Malami ya jagoranta.

Wakilan sun kawo ziyara ne jihar kan lamarin gobara da ta tashi a kasuwar Tudun-Wada dake babban birnin jihar, Gusau.

A cewar Matawalle, duk wasu tashe-tashen hankula da ke da alaƙa da ƙabilanci za'a iya kawar dasu ta hanyar tattaunawa, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa misalin tattaunawar da aka yi don kawo zaman lafiya a baya itace wacce aka yi da tsagerun Niger-Delta.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya roƙi FG tazo a yi taron sulhu da 'yan Ta'adda
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya roƙi FG tazo a yi taron sulhu da 'yan Ta'adda Hoto: @Bellomatawalle1
Source: Twitter

Kuma matukar aka yi irin wannan a yanayin da muke ciki na farmakin 'yan bindiga a jihar Zamfara da kuma yankin arewa maso yamma, to za'a kawo ƙarshen lamarin.

Ya kuma ƙara da cewa duk da gwamnatinsa na yaƙi da ta'addanci a jihar, kuma tana shirya tsaruka masu kyau ga matasa da mata musamman waɗanda rashin tsaron ya shafa.

A jawabin gwamnan yace:

"Kasan cewa mun yi imani da Allah, muna kallon wannan yanayin a matsayin jarabawa, Allah maɗaukakin sarki yace a cikin alƙur'ani 'Haƙiƙa zamu jarabeku da wani abu na tsoro, yunwa, asarar dukiya da rayuka, da kuma na kayan marmari, amma kayi bushara ga masu hakuri. Waɗanda idan musiba ta same su suke cewa: Tabbas, daga Allah muke, kuma tabbas izuwa gareshi muke komawa."

Gwamnan ya bayyana ma wakilan cewa gobarar ta laƙume shaguna 63 kuma yace ya naɗa kwamiti dazai gano waɗanda abun ya shafa.

KARANTA ANAN: 'Yan bindiga sun nemi a biya kudin fansan wadanda suka sace a Abuja har N200m

A bayaninsa, Malami ya yabawa gwamnan kan yadda yake kokarin fusakantar matsalar tsaron jihar, wanda yace yafara bada sakamako mai kyau.

Ministan ya kuma bayyana ƙudirin gwamnatin tarayya na haɗa hannu da gwamnatin jiha don taimakawa waɗanda lamarin gobarar ta shafa.

Ya kuma ƙara da cewa shugaban ƙasa ya bama ministar ma'aikatar jin ƙai da walwalar al'umma umarnin duba abubuwan da suka faru da kuma kawo agajin gaggawa ga ƴan kasuwar da lamarin ya shafa.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Source: Legit

Online view pixel