Da duminsa: APC zata yi gagarumin taron jam'iyya na kasa a watan Yuni, Badaru

Da duminsa: APC zata yi gagarumin taron jam'iyya na kasa a watan Yuni, Badaru

- Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya tabbatar da cewa za a yi taron jam'iyyar APC a watan Yuni

- Kamar yadda ya sanar da manema labarai, kwamitin rikon kwaryan ya shirya tsaf don sauke nauyin dake kansu

- Gwamnan yace a halin yanzu anyi wa mutane miliyan 36 rijistar jam'iyyar APC a fadin kasar nan

Gwamnan jihar Jigawa kuma shugaban kwamitin tsari na jam'iyyar APC, Badaru Abubakar, yace za a yi gagarumin taron jami'iyyar a watan Yuni.

Daily Trust ta ruwaito cewa, akwai rade-radin dake yawo na cewa za a kara wa'adin mulkin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a matsayin shugaban kwamitin tsari na jam'iyyar kuma za a kara lokacin taron ya wuce watan Yuni.

Amma a wata tattaunawa da manema labarai a sakateriyar jam'iyyar APC da yayi a ranar Talata, Badaru yace kwamitin rikon kwaryan ya shirya domin sauke nauyin dake kansu.

KU KARANTA: Fani Kayode ya musanta cin zarafin ma'aikatansa na cikin gidansa, ya garzaya gaban kotu

Da duminsa: APC zata yi gagarumin taron jam'iyya na kasa a watan Yuni, Badaru
Da duminsa: APC zata yi gagarumin taron jam'iyya na kasa a watan Yuni, Badaru. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Alaka da ƴan bindiga: Matawalle ya rantse da Qur'ani, ya bukaci ƴan jiharsa da su yi hakan

"Tabbas za a yi. Na san kwamitin riko kwaryan ya shirya zuwa watan Yuni kuma za mu goya musu baya tare da yin duk abinda ya dace domin ganin cewa mun sauke nauyin dake kanmu zuwa watan Yuni," yace.

Badaru yace APC ta yi wa mambobi miliyan 36 rijista a wannan sabunta rijistar 'ya'yan jam'iyyar da take yi kuma za a kammala zuwa ranar 31 ga watan Maris.

"Da farko mun buga na mambobi dubu goma sha biyu, amma yanzu haka mun wuce miliyan goma, mun kai miliyan 36. Hakan ba dole ya isa ba.

"A yanzu, muna cigaba da bugawa saboda idan mutane suna ganin ayyukan da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi fiye da mulkin da ya gabata, sai goyon bayan ya karu," yace.

A wani labari na daban, sama da fasinjoji 100 da za su je Legas suka sha dogon zama a filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano a ranar Lahadi bayan jirgin sama na Aero Contractors ya yi saukar gaggawa bayan mintuna kadan da tashinsa.

Kamar yadda ɗaya daga cikin fasinjojin dake jirgin ya sanar, jirgin ya tashi ne da karfe 9:30 na safe bayan an fara jin wata ƙara daga injin ɗin dama na jirgin wanda kusan dukkan fasinjojin suka ji.

Ya ƙara da cewa, jim kadan matuƙin jirgin ya sanar dasu cewa zai koma inda ya taso saboda ƙarar da ake ji.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel