Zulum ya sake bankado 'yan gudun hijira na bogi a sansanin Maiduguri
- Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum a daren Talata ya sake bankado mutum 528 na bogi a rijistar 'yan gudun hiijira
- Lamarin ya faru ne bayan ya kai ziyarar cikin dare sansanin inda ya kirga mazauna wurin daya bayan daya da kansa
- An gano cewa, daga cikin mutum 1316 da aka yi wa rijista suke karbar tallafi, 528 ba a sansanin suke ba
Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, ya gano mutane 528 dake ikirarin zama a sansanin 'yan gudun hijira na Maiduguri ba bisa ka'ida ba, jami'an gwamnatin jihar suka sanar.
Gwamnan ya kai ziyarar ba-zata ta cikin dare sansanin a ranar Talata inda ya kirga masu zama sansanin daya bayan daya.
Sansanin na kunshe da jama'a ne daga kananan hukumomin Bama, Koduga da Damboa na jihar Borno.
The Cable ta tattaro cewa a take Zulum ya rufe hanyar shiga sansanin bayan isar shi kuma da kanshi ya kirga jama'a.
KU KARANTA: Kwara: Rikici kan hijabi ya haɓaka, ƴan daba sun kai hari makarantu da kantuna
KU KARANTA: NDLEA ta Bankado Wata Tafkekiyar Gonar Wiwi a Jihar Kano
Kirgan ya bayyana cewa , daga cikin 1316 da jami'an tallafi da walwala suka bayyana, 528 duk na bogi ne. Mutum 788 ne kadai aka gani ido da ido a cikin sansanin.
Gwamnan yace an yi wannan kirgan ne domin shawo kan matsalar mazauna yankin dake morewa daga kayayyakin 'yan gudun hijarar.
Jami'an gwamnatin jihar Borno wadandaa suka taya gwamnan kirgar sun ce Zulum baya bakin cikin jama'a su samu tallafi, amma baya son 'yan damfara na kwashe kayan 'yan gudun hijirar.
A kwanakin baya ne Zulum ya bankado mutum 650 na bogi a sansanin 'yan gudun hijira dake kwalejin karantun shari'ar Musulunci ta Mohammed Goni dake Maiduguri.
A wani labari na daban, a jiya ne wasu dattawan arewa suka yi magana a kan abinda suka kwatanta da kokarin illatawa tare da raunata arewa ta hanyar nuna cewa dukkan abubuwa marasa dadi dake faruwa na da alaka da yankin kafin zuwan zaben 2023.
Dattawan karkashin kungiyar dattawan arewa (NEF) sun ce abubuwa miyagu dake faruwa a kasar nan sakamako ne na masu mulki da suka kasa baiwa 'yan Najeriya kariya.
A wata takardar da aka turawa Leadership a Abuja, Dr Hakeem Baba-Ahmed, daraktan yada labarai na kungiyar, yace NEF na zargin cewa dukkan abubuwan dake faruwa ana yinsu ne don birkita 2023.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng