Kwamishina ya fara aiki a karkashin bishiya saboda babu ofishin da zai shiga a Taraba

Kwamishina ya fara aiki a karkashin bishiya saboda babu ofishin da zai shiga a Taraba

- A jihar Taraba lamarin ya kai an nada Kwamishina babu ofishin da zai shiga

- Jethro Yakubu zai rika aiki a karkashin bishiya ne kafin ya samu wurin zama

- An rusa ofisoshin ma’aikatar ne lokacin da aka yi ta zanga-zangar #EndSARS

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa sabon kwamishinan kawar da talauci na jihar Taraba, Mista Jethro Yakubu ya shiga ofis bayan an rantsar da shi.

Rahotanni sun ce Jethro Yakubu ya soma aiki ne a ranar Laraba, 24 ga watan Maris, 2021.

Abin mamakin shi ne Mista Yakubu ya fara aikinsa ne a karkashin bishiya bayan sakadaren din-din-din na ma’aikatar jihar ya mika masa ragamar aiki.

KU KARANTA: Matan da su ka zama manyan Jami’ai a aikin khaki a Najeriya

Da yake jawabi a ranar Laraba a garin Jalingo, Jibrin Na Wukari ya ce sun shafe kusan watanni shida su na aiki a haka, watau a karkashin wannan bishiya.

Mista Na Wukari ya ke cewa abin takaici ne ace ma’aikatar da ta ke da nauyin kawar da talauci a jihar Taraba, ta na aiki a cikin wani irin yanayi na kaskanci.

Sakataren din-din-din na ma’aikatar ya roki sabon kwamishinan ya taimaka wajen ganin ya yi abin da ya dace domin a samu dakunan da za a rika yin aiki.

An rusa ofisoshin ma’aikatar ne a lokacin da aka yi zanga-zangar #EndSARS a watan Oktoban 2020.

KU KARANTA: Rochas Okorocha zai gina makarantun Almajirai

Kwamishina ya fara aiki a karkashin bishiya saboda babu ofishin da zai shiga a Taraba
Jethro Yakubu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“A nan mu ke zama a kullum, kuma ga shi yanzu lokacin damina ya zo, ka da ka yi mamaki ka zo wurin aiki, ka samu babu wanda ya zo ofis.” Inji Na Wukari.

Ya ce: “Babu wani lafiyayyen ofishi a nan. Mu na fata tun da ka zo, gwamnan jiha zai yi abin da ya dace, sannan mu iya samun damar yin aiki cikin jin dadi.”

Ku na da labarin irin ta'adin da aka yi da sunan zanga-zangar #EndSARS aka shirya a 2020. Hakann ya sa wasu gwamnoni su ka ja-kunnen matasansu.

Mai Mala Buni ya yi kira ga matasan Yobe da na yankin Arewa maso gabashin Najeriya su kaurace wa zanga-zangar, Abdullahi Sule ya yi irin wannan kira.

A lokacin da aka yi wannan zanga-zangar, matasa sun rusa ofisoshin ma’aikatar, su ka lalata kayan aiki har da na’urar bada iska watau AC da kuma teburori.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng