Rundunar Yan sanda na neman wasu Mutane 18 Ruwa a jallo a Jihar Ebonyi

Rundunar Yan sanda na neman wasu Mutane 18 Ruwa a jallo a Jihar Ebonyi

- Rundunar 'yan sanda a jihar Ebonyi sun bayyana sunan wasu mutane 18 da suke nema ruwa a jallo.

- Yan sandan sun bayyana cewa suna zargin mutanen da hannu a tayar da tashe-tashen hankula tsakanin ƙabilu.

- Jami'i mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya aike ma yan Jarida ranar Talata.

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Ebonyi sun bayyana wasu mutane 18 da suke nema ruwa a jallo da zargin rura wutar rikici tsakanin al'umma.

KARANTA ANAN: Zulum ya sake bankado 'yan gudun hijira na bogi a sansanin Maiduguri

Wannan sanarwa na ɗauke ne a wani saƙo da jam'i mai magana da yawun yan sandan jihar, DSP Loveth Odah, ya aike ma yan jarida ranar Talata, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Sanarwar ta bayyana cewa ana neman mutanen ne sabida zargin su da aikata kisan kai, kunna wuta, ƙungiyar asiri da kuma ta'amali da makamai ba bisa ƙa'ida ba.

DSL Loveth Odah yace mutanen sune:

"Sunayen mutanen sune Nwankwo Godwin wanda akafi sani da AKA, Hope Nwankwo, Chibueze Nwifuru wanda akafi sani babban nama, da kuma Daniel Nwangwoto."

KARANTA ANAN: Kyawawan hotunan sarakuna 3 masu karancin shekaru a Najeriya da cikakken tarihinsu

"Sauran sun haɗa da Osondu Mgbada (AKA taɓo), Okechukwu Nwanga (AKA Ezza), Chukwudi Nwite (AKA ɗan auta), Ernest Aduma, Chukwudi Okefi (AKA Mala'ika), Oliver Okefi (AKA Malife), Osondu Okefi da kuma Elom John," inji shi.

Rundunar Yan sanda na neman wasu Mutane 10 Ruwa a jallo a Jihar Ebonyi
Rundunar Yan sanda na neman wasu Mutane 10 Ruwa a jallo a Jihar Ebonyi Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

"Paul Elom, Odinaka Idu, Monday Idu, Solomon Okefi, Chinedu Ilor da kuma Garba duk suna daga cikin waɗanda muke nema," a cewarsa.

A wani labarin kuma Gwamnan Zamfara ya ƙara samun nasarar kuɓutar da wasu mutane huɗu da aka sace

Waɗanda aka kuɓutar din sun bayyana cewa an sace su kwana 49 da suka wuce a garin Boko dake ƙaramar hukumar Zurmi, jihar Zamfara.

Daga cikin waɗanda gwamnan ya kuɓutar akwai Magajin Gari da kuma kansila daga ƙaramar hukumar Zurmi.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262