Masu Baburan Adaidaita Sahu Sun Shiga Yajin Aiki a Maiduguri
- Masu baburan adai-daita sahu sun shiga yajin aiki a birnin Maiduguri, jihar Borno
- Masu adai-daita sahun sun ce shiga yajin aikin ne saboda cin mutuncin da jami'an gwamnati ke musu
- Sun yi ikirarin cewa ana musguna musu wurin karbar haraji sannan jami'an gwamnatin na wuce gona da iri yayin aiki
Daruruwan masu baburan adaidaita-sahu da aka fi sani da Keke-Napep sun kauracewa tituna a Maiduguri sakamakon yajin aikin da suka fara kan abinda suka kira cin mutunci da jami'an gwamnati ke musu.
Fasinjoji da dama sun rasa abubuwan hawa zuwa wuraren da za su tafi yayin da yara yan makaranta suka rika takawa suna tafiya mai nisa domin zuwa makaranta, Daily Trust ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Angon Da Ya Auri Matar Da Aka Saka Wa Rana Da Ƙaninsa, Soja, Da Ya Mutu Ya Magantu
Daya daga cikin direbobin a titin Baga, Usman Modu, ya ce direbobin suna biyan N100 na haraji a kullum, 'amma idan aka jinkirta biyan zuwa wani lokaci sai a yi kari a kai matsayin tara idan kuma ka kasa biya sai a kwace makullin ka.
"Suna cin mutuncin mu saboda tufafinmu, misali idan ka saka riga mara hannu toh ranan ba za a bari kayi aiki ba.
"Masu karbar harajin ma suna wuce gona da iri suna tambayan lasisin tuki wanda ba ya cikin aikinsu."
KU KARANTA: Irabor: Ƴan Boko Haram 500 Suna Gidan Yari, Wasu Za Su Shafe Shekaru 60 a Ɗaure
Dukkan kokarin da aka yi na ji ta bakin jami'in karamar hukuma na gwamnatin jihar ya ci tura.
Wata daliba a Ibrahim Taiwo Estate ta ce ta yi tafiya mai nisa zuwa makaranta.
A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.
An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.
Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng