Jerin Ƙasashen Duniya 10 Mafi Hatsarin Zama a Shekarar 2021

Jerin Ƙasashen Duniya 10 Mafi Hatsarin Zama a Shekarar 2021

Rahoton GPI ya yi nazarin kasashen duniya 163 da suka kunshi kashi 99 cikin 100 na mutanen duniya. An kasa abubuwan da aka yi nazari zuwa gida uku; Tsaro da Zaman Lafiya, Rikici da ya gaza karewa da zama cikin shirin yaki.

Jerin Kasashe 10 Mafi Matsari a Fadin Duniya a Shekarar 2021
Jerin Kasashe 10 Mafi Matsari a Fadin Duniya a Shekarar 2021. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mutum 19 Sun Rasu, 34 Sun Jikkata Sakamakon Hatsarin Mota a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Ga jerin kasashen duniya goma mafi hatsari kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

1. Afghanistan

Afghanistan ne kasa mafi hatsari a duniya a cewar alkalluman Global Peace Index ta shekarar 2019. A cewar Dakarun Samar da Zaman Lafiya na UN a Afghanistan, fararen hula 3,804 sun mutu a jihar saboda rikici, 927 cikinsu yara ne. Taliban na kai hare-hare a sassan kasar sannan a yanzu shekaru 19 kenan Afghanistan na yaki da Amurka. Baba wata kasa a duniya da ta fi rasa mutane fiye da Afghanistan sakamakon yaki da ta'addanci.

2. Syria

Syria ce kasa ta biyu mafi hatsari a duniya. Yakin basasa ya adabi kasar tun Maris din 2011. A kalla mutane 470,000 cikinsu da yara 55,000 suka mutu sakamakon rikicin. Ana cigaba da rikici a kasar ta hanyar amfani da kananan makamai, tankunan yaki, sinadarai masu guba, jiragen yaki da sauransu.

3. Iraq

Iraqi ce ke biye da Syria a jerin kasashe mafi hatsari. Iraq na cigaba da fuskantar rikicin cikin gida na da waje. ISIS na cigaba da kashe farar hula da sojojin kasar. Ana kuma cigaba da keta hakkin bil adama.

4. South Sudan

South Sudan ce kasa ta hudu mafi hatsari a duniya. An dade ana rikici a South Sudan da suka hada da karuwar muggan laifuka da suka hada da fashi, kwace, satar mota, garkuwa da mutane da sauransu. An dade ana yaki tsakanin gwamnati da kungiyoyi masu adawa da gwamnatin hakan yasa babu doka sosai a kasar baya ga babban birnin jihar Juba.

5. Yemen

Kasa ta biyar a wannan jerin itace Yemen. An fara yakin basasa na Yemen a 2015 tsakanin bangarori biyu. Gwamnatin Abdrabbuuh Mansur Hadi da yan kungiyar Houthi. Yemen ne ke da rikicin al'umma mafi muni a duniya a cewar UN bayan shekaru hudu ana rikici a kasar hakan yasa mutanen miliyan 4.3 suka bar gidajensu, wasu miliyan 14 suna fuskantar barazanar yunwa da barkewar cututuka masu kisa. Kimanin kashi 80 cikin 100 na kasar (miliyan 24) na bukatar taimako.

6. Somalia

Akwai barazanar sace mutane a dukkan sassan Somalia. Akwai yiwuwar harin ta'addanci a filin tashin jirage na Mogadishu, gine-ginen gwamnati, otal da wuraren cin abinci. Karancin abinci da rashin tsaro da yanayi mai kyau yana kara asassa matsalar.

KU KARANTA: 2023: Zan 'Raba Jiha' Da Jonathan Muddin Ya Ce Zai Yi Takara a APC, Wike

7. Libya

Libya ce kasa ta bakwa mafi hatsari a duniya. Akwai manyan laifuka da suka hada da garkuwa da mutane, rikici tsakanin kungiyoyi, ta'addanci da sauransu a kasar. Mafi yawancin rikicin Libya ya samo asali ne saboda fada tsakanin kungiyoyin yan bindiga. ISIS ta sha kai hare-hare a kasar.

8. Democratic Republic of the Congo (Jamhuriyar Demokradiya ta Congo, DRC)

DRC ce kasa ta takwas a wannan jerin. A baya bayan nan ne annobar Ebola ta yi wa kasar barna inda fiye da 2,200 suka mutu a cewar Kungiyar Lafiya ta Duniya, WHO. A kan yawan yin zanga-zanga a kasar da ke rikidewa ta zama rikici. Muggan laifuka sun yi yawa a kasar da suka hada da fashi, sata, da rashin isasun hukumomin tsaro.

9. Central African Republic (CAR)

CAR ce kasa ta tara mafi hatsari a duniya. Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattaba hannu a kai a 2017, an cigaba da samun rikici a kasar. Mafi girma cikin rikicin shine fada tsakanin Yan tawayen Seleka da Anti-Balaka. Rikicin ya saka mutane kimanin 620,000 sun rasa muhallinsu ya kuma saka yan gudun hijira 570,000 suka bar kasar zuwa kasashen da ke makwabtaka. Akwai yawan laifuka kamar sata, keta hakkin bil adama da sauransu.

10. Russia (Rasha)

Russia ce kasa ta 10 mafi hatsari a duniya. Yawan makaman da Russia ke da shi ya taka rawa wurin saka ta cikin wannan jerin kasashen masu hatsari. Akwai yiwuwar kungiyoyin yan ta'adda na gida da kasashen ketare su iya shiga Russia da kuma mutane masu tsatauran ra'ayi. Jami'an Russia kuma a wasu lokutan suna tsare yan asalin kasar Amurka.

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel