Hotunan Sabon Katafaren Gidan Da Ɗan Uwan Buhari Ya Gina A Abuja

Hotunan Sabon Katafaren Gidan Da Ɗan Uwan Buhari Ya Gina A Abuja

- Fatuhu Mohammed, Dan majalisar tarayya mai wakiltar, Daura/Maiadua/Sandamu ya nuna hoton sabuwar gidan da ya gina a Abuja

- Dan majalisar wanda dan uwa ne ga Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci mutane su taya shi murna game da kammala ginin gidan

- A cewar Fatuhu Mohammed, ya dauki kimanin tsawon shekaru hudu kafin kammala ginin dankareran gidan da yace a Gwarimpa Abuja ya gina

Dan uwan Shugaba Muhammadu Buhari kuma dan majalisar wakilai na tarayya, Fatuhu Muhammed ya nuna sabuwar katafaren gidan da ya gina a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Muhammed, wanda ke wakiltar mazabun Daura/Maiadua/Sandamu a karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress APC, ya ce ya gina gidan ne a cikin shekaru hudu.

DUBA WANNAN: Ku Shirya Birne Nigeria idan Ku Ka Kashe Ortom: Wike Ya Gargaɗi FG

Hotunan Sabon Katafaren Gidan da Ɗan Uwan Buhari Ya Gina A Abuja
Hotunan Sabon Katafaren Gidan da Ɗan Uwan Buhari Ya Gina A Abuja. Hoto: Hon. Fatuhu Mohammed
Source: Facebook

Dan majalisar ya nuna hotunan katafaren gidan alfarmar a shafinsa na dandalin sada zumunta na Facebook inda ya bukaci abokansa da masoya su taya shi da addu'ar nasarar abinda ya cimma.

Hotunan Sabon Katafaren Gidan da Ɗan Uwan Buhari Ya Gina A Abuja
Hotunan Sabon Katafaren Gidan da Ɗan Uwan Buhari Ya Gina A Abuja. Hon Fatuhu Mohammed
Source: Facebook

"Alhamdullilah, na kammala gina gida na a Gwarimpa (Abuja) da ya dauke ni kimanin shekaru hudu ginawa amma don haka dukkan godiya ta tabbata ga Allah kuma ina bukatar addu'o'in ku.

KU KARANTA: Saraki Ya Roki Ƴan Nigeria Su Sake Bawa PDP Dama a 2023

"Zan sanar da ranar tarewa a gidan nan gaba," ya rubuta.

Jim kadan bayan wallafa sakon, dan majalisar ya cire hotuna da rubutun da ya wallafa.

A watan Satumban shekarar da ta gabata, Mr Fatuhu ya yi barazanar harar wani mai amfani da Facebook, mai suna Abdulbasi Maiadua saboda ya soke shi.

Dan majalisar ya yi barazanar ne cikin hirar wayar tarho da aka nada inda ya ke cewa, "ina son ka nada wannan maganar. Ina yi maka gargadi, ni ba tsaran ka bane, kuma ni ba mai gidan ka bane. Idan baka fita daga harkokina ba, zan yi maganin ka. Kana iya kai kara wurin duk wanda kake so a Katsina ko kuma a Nigeria."

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel