Akeredolu ga masu son kafa kasar Oduduwa ta Yarbawa: Ku nisanci jiha ta

Akeredolu ga masu son kafa kasar Oduduwa ta Yarbawa: Ku nisanci jiha ta

- Gwamna jihar Ondo ya gargadi Sunday Igboho kan batun kafa haramtacciyar kasar Yarbawa

- Gwamnan ya bayyana cewa, jiharsa bata amince da shawarar ballewa daga Tarayyar Najeriya ba

- Ya kuma jadda cewa, jiharsa ba za ta taba yarda da taron sakarci da ganganci irin na Igboho ba

Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya gargadi Sunday Igboho da wasu da ke neman kafa haramtacciyar kasar Yarbawa da su nisanci jiharsa, The Nation ta ruwaito.

Akeredolu ya ce mutanen Ondo sun zabi zama a Tarayyar Najeriya dunkulalliya kamar yadda aka tsara tun farkon kafa Najeriya.

Ya ce babu wani yanki na jihar, da aka sani kuma aka ayyana shi a matsayin jihar Ondo, da zai ba da izinin wani taro ko tashin hankali wanda zai iya ba da shawara ta kusa ko nesa, cewa mutane suna goyon bayan abin da ya kira 'rudani mai rudarwa.'

Akeredolu wanda ya yi magana yayin rantsar da Gimbiya Catherine Oladunni Odu a matsayin sabuwar Sakatariyar Gwamnatin Jihar da sauran masu ba da shawara na musamman ya ce jihar ba za ta yarda da barnar tsageru da sakacinsu ba.

KU KARANTA: Gandollar: Idan wani abu ya same ni, a tuhumi Ganduje, Jaafar Jaafar ga IGP

Akeredolu ga masu son kafa kasar Oduduwa ta Yarbawa: Ku nisanci jiha ta
Akeredolu ga masu son kafa kasar Oduduwa ta Yarbawa: Ku nisanci jiha ta Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Akeredolu ya jaddada cewa duk wadanda abin ya shafa dole ne su amince da bin manufofi iri daya don isa ga manufa daya.

Igboho kwanan nan ya ayyana kafa haramtacciyar kasar Yarbawa, yana mai ikirarin cewa jihohin Kudu maso Yammacin Najeriya yanzu ba yanki ne na Najeriya ba.

Ya bukaci dukkan ‘yan asalin Yarbawa wadanda ke zaune a jihohin Hausa/Fulani ko Ibo, da su dawo gida kafin yaki ya barke.

Ya kara da cewa duk wani sarkin Yarabawa da ya musanta goyon bayan kungiyarsa mai fafutukar ‘yantar da Kudu maso Yamma ba zai 'ga hasken gobe ba.’

A cewarsa, “Me yasa muke bayi a kasarmu ta gado? Me yasa ake bautar damu a kasarmu?

KU KARANTA: Iyayen dalibai sun bai wa El-Rufa'i wa'adin awanni 48 ya dawo musu da 'ya'yansu

A wani labarin, Wani tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai kuma jigo a jam'iyyar APC, Sanata Abu Ibrahim, ya ce Najeriya za ta zauna lafiya a karkashin Asiwaju Bola Tinubu, idan aka zabe shi a matsayin Shugaban kasa a zaben 2023.

Tsohon sanatan dan asalin jihar Katsina yayi wannan maganan ne a karshen mako a Abuja yayin kaddamar da kungiyar nuna goyon bayan Bola Tinubu (BTSO), The Nation ta ruwaito.

Ya nuna goyon baya ga masu tallata shugabancin Bola Tinubu a 2023, yana mai cewa ya san Shugaban na APC na Kasa sama da shekaru 20.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel