Kyawawan hotunan sarakuna 3 masu karancin shekaru a Najeriya da cikakken tarihinsu

Kyawawan hotunan sarakuna 3 masu karancin shekaru a Najeriya da cikakken tarihinsu

Najeriya tanada da masu sarautar gargajiya wadanda suke rike da al'adu tare da sarautar yankunansu. Yayin da yawancinsu tsofaffi ne, akwai sarakuna uku da ake kwatantawa da wadanda suka fi dukkansu yarinta.

1. Mai Martaba Obi Chukwuka Noah Akaeze

Tun farko ya kasance sarki mafi karancin shekaru a Najeriya bayan mutuwar mahaifinsa da ya gada. Ya karba mulkin masarautar Ubulu-Uku dake karamar hukumar Aniocha ta jihar Delta tun yana da shekaru 18 a 2016.

Kamar yadda jaridar The Guardian ta tabbatar, ya karba ma'aikatansa a ranar Litinin, 5 ga watan Satumban 2016 daga gwamnatin jihar kuma an yi gagagrumin bikin nadiin sarautarsa.

A 2019, ya kammala digirinsa daga wata jami'a daka Ingila inda ya karanta shari'a. A halin yanzu basaraken yana da shekaru 23 a duniya.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sheke 'yan sanda 3 a Abia, sun yi awon gaba da bindigogi

Kyawawan hotunan sarakuna 3 mafi karancin shekaru a Najeriya da cikakken tarihinsu
Kyawawan hotunan sarakuna 3 mafi karancin shekaru a Najeriya da cikakken tarihinsu. Hoto daga Igwebuike Igbo Youth Association of Nigeria
Asali: Facebook

2. Oloyede Adeyeoba Oloyede

An zabi Adeyeoba a matsayin sarki Arujale na Okeluse dake karamar hukumar Ose ta jihar Ondo a 2020 yayin da yake da shekaru 15 a duniya.

Basaraken, wanda yanzu shekarunsa na haihuwa 16, yana babbar makarantar sakandare ne kuma shi kadai ne magajin mahaifinsa.

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ne ya nada shi bayan tantancesu da aka yi a karkashin kwamitin nadin sarakuna.

3. Akubuisi Okonkwo

Yana da shekaru 10 da haihuwa, an nada Akubuisi Okonkwo a matsayin sarkin masarautar Iyiora Anam dake karamar hukumar Anambra ta yamma a jihar Anambra.

Kamar yadda Correct NG ta wallafa, an yi nadin a ranar Alhamis, 27 ga watan Janairun 2020 bayan rasuwar mahaifinsa mai martaba Igwe Onyeachonam Okonkwo, Olame 1 na Aiyiora Anam.

Kyawawan hotunan sarakuna 3 mafi karancin shekaru a Najeriya da cikakken tarihinsu
Kyawawan hotunan sarakuna 3 mafi karancin shekaru a Najeriya da cikakken tarihinsu. Hoto daga correct.Ng
Asali: UGC

KU KARANTA: 2023: Dattawan arewa na zargin ana shiryawa yankin wata maƙarƙashiya

A wani labari na daban, rikicin hijabi da yaki ci balle cinyewa a jihar Kwara a jiya ya karu kuma ya sauya salo yayin da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai hari makarantu da kantuna a Ilorin, babban birnin jihar.

Yankunan Kiristoci, tsoffin mamallakan makarantu 10 da gwamnati ke tallafawa, sun samo jami'ai da suka kare harin duk don kokarinsu na baiwa jama'a da dukiyoyi kariya.

Kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa, daukin da jami'an 'yan sanda, NSCDC da dakarun sojin Najeriya suka kai ne yasa lamarin bai tsananta ba.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng