Kwara: Rikici kan hijabi ya haɓaka, ƴan daba sun kai hari makarantu da kantuna

Kwara: Rikici kan hijabi ya haɓaka, ƴan daba sun kai hari makarantu da kantuna

- Wasu miyagu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari makarantu da kantuna a jihar Kwara

- Bata-garin sun yi hakan ne duk a cikin rikicin sanya hijabi ga 'yan makarantar jihar da gwamnan yasa

- An gano cewa taimakon jami'an 'yan sanda, NSCDC da na sojojin Najeriya ne yasa lamarin bai yi kamari ba

Rikicin hijabi da yaki ci balle cinyewa a jihar Kwara a jiya ya karu kuma ya sauya salo yayin da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai hari makarantu da kantuna a Ilorin, babban birnin jihar.

Yankunan Kiristoci, tsoffin mamallakan makarantu 10 da gwamnati ke tallafawa, sun samo jami'ai da suka kare harin duk don kokarinsu na baiwa jama'a da dukiyoyi kariya.

Kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa, daukin da jami'an 'yan sanda, NSCDC da dakarun sojin Najeriya suka kai ne yasa lamarin bai tsananta ba.

KU KARANTA: Ba za mu bada kunya ba, dukkan kallo ya dawo kanmu, Shugaban EFCC Bawa

Kwara: Rikici kan hijabi ya haɓaka, ƴan daba sun kai hari makarantu da kantuna
Kwara: Rikici kan hijabi ya haɓaka, ƴan daba sun kai hari makarantu da kantuna. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Barnar tsuntsaye ta ja jirgin sama da zai je Legas saukar gaggawa a Kano

An gano cewa 'yan daban sun bayyana da miyagun makamai da suka hada da adduna tare da kwalabe yayin da suke tattaki a manyan titunan birnin Ilorin.

Wasu 'yan daba da aka gani a wurin titin Offa dake GRA Ilorin sun saka takunkumin fuska domin boye kansu.

Kamar yadda ganau ba jiyau ba suka tabbatar, 'yan daban sun dinga jefa duwatsu farfajiyar makarantar Cherubim and Serphim dake Sabo-Oke a kokarinsu na bude kofar makarantar da karfi.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya karba bakuncin Oladimeji Bankole, tsohon kakakin majalisar wakilai da Gbenga Daniel, tsohon gwamnan jihar Ogun a fadarsa dake Abuja.

Bankole da Daniel cikin kwanakin nan ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Yayin kai ziyarar fadar shugaban kasa, sun samu rakiyar Mai Mala Buni, Mohammed Badaru da Atiku Bagudu, gwamnonin Yobe, Jigawa da Kebbi.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel