2023: Dattawan arewa na zargin ana shiryawa yankin wata maƙarƙashiya

2023: Dattawan arewa na zargin ana shiryawa yankin wata maƙarƙashiya

- Kungiyar dattawan arewa ta zargi wasu 'yan siyasa da shiryawa yankin maƙarƙashiya kafin 2023

- Kakakin kungiyar, Dr Hakeem Baba-Ahmed, yace hakan ba zai sa arewa ta hakura da burikanta da ta sa gaba ba

- Kamar yadda dattawan suka sanar, yankin arewa na fatan Najeriya ta zama kasar da ba a baiwa wata kungiya fifiko

A jiya ne wasu dattawan arewa suka yi magana a kan abinda suka kwatanta da kokarin illatawa tare da raunata arewa ta hanyar nuna cewa dukkan abubuwa marasa dadi dake faruwa na da alaka da yankin kafin zuwan zaben 2023.

Dattawan karkashin kungiyar dattawan arewa (NEF) sun ce abubuwa miyagu dake faruwa a kasar nan sakamako ne na masu mulki da suka kasa baiwa 'yan Najeriya kariya.

A wata takardar da aka turawa Leadership a Abuja, Dr Hakeem Baba-Ahmed, daraktan yada labarai na kungiyar, yace NEF na zargin cewa dukkan abubuwan dake faruwa ana yinsu ne don birkita 2023.

KU KARANTA: Alaka da ƴan bindiga: Matawalle ya rantse da Qur'ani, ya bukaci ƴan jiharsa da su yi hakan

2023: Dattawan arewa na zargin ana shiryawa yankin wata maƙarƙashiya
2023: Dattawan arewa na zargin ana shiryawa yankin wata maƙarƙashiya. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Alaka da ƴan bindiga: Matawalle ya rantse da Qur'ani, ya bukaci ƴan jiharsa da su yi hakan

Dattawan sun ce duk wadanda suka yadda cewa zasu iya tsoratawa ko barazana ga arewa domin su mika kai tare da hakura da bukatunsu na tafka babban kuskure.

Sun ce arewa na bukatar Najeriya ta kasance kasar da za ta iya shawo kan kananan matsalolinta masu tarin yawa.

NEF tace kamar sauran 'yan Najeriya, ta yadda cewa babu wata kungiya da za a baiwa fifiko fiye da wata.

A yayin jawabi, kakakin kungiyar, Baba-Ahmed, ya ja kunnen cewa kafin zuwan 2023, babu wani salo na damokaradiyya da miyagun 'yan siyasa marasa hangen nesa zasu dakile.

A wani labari na daban, sama da fasinjoji 100 da za su je Legas suka sha dogon zama a filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano a ranar Lahadi bayan jirgin sama na Aero Contractors ya yi saukar gaggawa bayan mintuna kadan da tashinsa.

Kamar yadda ɗaya daga cikin fasinjojin dake jirgin ya sanar, jirgin ya tashi ne da karfe 9:30 na safe bayan an fara jin wata ƙara daga injin ɗin dama na jirgin wanda kusan dukkan fasinjojin suka ji.

Ya ƙara da cewa, jim kadan matuƙin jirgin ya sanar dasu cewa zai koma inda ya taso saboda ƙarar da ake ji.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel