Irabor: Ƴan Boko Haram 500 Suna Gidan Yari, Wasu Za Su Shafe Shekaru 60 a Ɗaure

Irabor: Ƴan Boko Haram 500 Suna Gidan Yari, Wasu Za Su Shafe Shekaru 60 a Ɗaure

- Rundunar sojojin Nigeria ta ce a kalla yan Boko Haram 500 suna daure a gidan yari

- Rundunar ta ce wasu daga cikinsu an yanke musu hukuncin dauri har na shekaru 60

- Babban hafson tsaro na Nigeria, Lucky Irabor ne ya sanar da hakan yayin wani taro da aka yi

Lucky Irabor, Babban Hafson Tsaron Nigeria ya ce fiye da yan Boko Haram 500 ne suke tsare a gidan gyaran hali tun bayan kaddamar ta shirin Safe Corridor, rahoton The Cable.

Rundunar Sojin ta kaddamar da Safe Corridor, da nufin sauya tunanin tsaffin yan ta'addan ne tun shekarar 2016.

Irabor: Yan Boko Haram 500 Suna Gidan Yari, Wasu Za Su Shafe Shekaru 60 Daure
Irabor: Yan Boko Haram 500 Suna Gidan Yari, Wasu Za Su Shafe Shekaru 60 Daure. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mutum 19 Sun Rasu, 34 Sun Jikkata Sakamakon Hatsarin Mota a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

A cewar sojin, nufin shirin shine mayar da tubabbin yan Boko Haram cikin jama'a. Tsaffin yan Boko Haram fiye da 500 sun kammala shirin.

Da ya ke magana wurin taron da aka yi wa lakabi da “The North-East Symposium on Reintegration, Reconciliation and Resettlement,” a ranar Litinin, Irabor wanda ya samu wakilcin Bamidele Ashafa ya ce an gurfanar da yan ta'adda fiye da 1000.

Ya ce wasu daga cikinsu an musu daurin shekaru 60 a gidan gyaran hali.

"Gwamnatin tarayya bata karfafawa Boko Haram gwiwa. An gurfanar da yan Boko Haram fiye da 1,000. Ina son amfani da wannan damar in sanar da cewa fiye da 500 suna daure a gidan yari cikinsu akwai wadanda za su yi shekaru 60, mafi karancin daurin shine na shekaru 5," in ji shi.

KU KARANTA: Jerin Ƙasashen Duniya 10 Mafi Hatsarin Zama a Shekarar 2021

Mutane da dama sun nuna rashin goyon bayansu da tsarin na sauya tunanin yan ta'addan.

Babagana Zulum, gwamnan Borno ya ce tubabbun yan bindigan sukan zama yan leken asiri su sake komawa kungiyar bayan sauya musu tunanin.

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel