Gwamnati Za Ta Iya Dena Biyan Tallafin Lantarki a Karshen 2021, In Ji Hadimin Buhari

Gwamnati Za Ta Iya Dena Biyan Tallafin Lantarki a Karshen 2021, In Ji Hadimin Buhari

- Akwai yiwuwar gwamnatin tarayya za ta dena biyan tallafin kudin lantarki a karshen shekarar 2021

- Ahmed Zakari, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman ne ya sanar da hakan yayin wata taro a Abuja

- Zakari ya ce dena biyan tallafin ba zai saka farashin lantarkin ya yi tsada ba muddin ana samar da isasshen lantarkin

Ahmed Zakari, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa kan gine-gine, ya ce akwai yiwuwar gwamnatin tarayya za ta dena biyan tallafin kudin lantarki a karshen shekarar 2021, The Cable ta ruwaito.

A yayin jawabin da ya yi yayin taron Cibiyar Cinikayya da Kasuwanci (AICC) ta shirya ta yanar gizo, Zakari ya ce cire tallafin zai inganta samar da wutar lankarki.

Gwamnati Za Ta Iya Dena Biyan Tallafin Lantarki a Karshen 2021, In Ji Hadimin Buhari
Gwamnati Za Ta Iya Dena Biyan Tallafin Lantarki a Karshen 2021, In Ji Hadimin Buhari. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bashir Dandago: Hukumar Tace Fina-Finai a Kano Ta Kama Mai Waƙoƙin Yabon Annabi

This Day ta ruwaito cewa hadimin shugaban kasar ya ce ana hasashen hukumar samar da lantarki ta kasa (NESI) za ta samar da N100 biliyan zuwa tsakiyar shekara.

"Da wannan sabon tsarin amfani da na'urar mita, muna hasashen NESI za ta iya samar da fiye da N100 biliyan zuwa tsakiyar shekara. Wannan abin yabawa ne," in ji Zakari.

"Hasashen da muke yi shine idan ka inganta hanyar da masu amfani da wuta za su biya kudinsu ta hanyar samar musu da mita, kudin shiga zai karu. Mun nuna hakan.

KU KARANTA: Jerin Ƙasashen Duniya Goma Mafi Hatsari a Shekarar 2021

"Muna shirin janye tallafin lantarki zuwa karshen shekara. Wasu za su ce idan ka cire tallafi, kudin da talaka ke biya zai karu. Amma abinda muke gani shine dalilin da yasa lantarki ke tsada shine ba mu samar da isashe.

"Idan kana samar da 10 GW na lantarki, kudinsa zai rage zuwa rabi. Don haka rage kudin ba shine abinda ya fi ba amma samar da isashen lantarkin."

A watan Fabrairu, Saleh Mamman, Ministan Makamashi ya ce gwamnatin tarayya na kashe fiye da Naira miliyan 50 duk wata a kan tallafin kudin lantarki.

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel