Shugaban kasa Buhari zai jagoranci bikin Maulidin Jagoran APC, Tinubu na 2021
- Shugaban kasa aka zaba ya jagoranci bikin Bola Tinubu Colloquium-12
- A shekarar bana ne Bola Ahmed Tinubu ya ke cika shekara 69 a Duniya
- Ana sa ran Muhammadu Buhari ya halarci taron da za ayi shekarar nan
Jaridar Punch ta ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai shugabanci taron bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
A ranar Litinin dinnan mai zuwa, wanda zai kama 29 ga watan Maris, 2021, za ayi bikin taya Asiwaju Bola Tinubu murnar cika shekaru 69 a Duniya.
A shekarar bana za ayi bikin Bola Tinubu Colloquium, wannan shi ne karo na 12 da za a gudanar.
KU KARANTA: Jigon CPC ya na so mutumin Kudu ya gaji kujerar Shugaban kasa
Rahotanni sun tabbatar da cewa mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari da kan shi ne zai jagoranci wannan katafaren biki da za ayi ta kafar yanar gizo.
Wannan shekarar, ofishin mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne zai dauki dawainiyar bikin taya babban ‘dan siyasar kasar murna.
Taken bikin da za ayi wannan shekarar shi ne: ‘Our Common Bond, Our Common Wealth: The Imperative of National Cohesion for Growth and Prosperity’.
Za a tattauna game da tasirin hadin-kan Najeriya wajen cigaban kasar a wajen bikin shekarar bana.
KU KARANTA: 'Dan Hadimar Aisha Buhari ya nunawa Duniya motar da ya saya
Hakan ya na zuwa ne a lokacin da wasu su ke rade-radin cewa alakar Bola Tinubu da shugaba Muhammadu Buhari ta cabe tun bayan da aka yi zaben 2023.
Duk shekara a kan gudanar da wannan taro da ya kan samu halartar manyan ‘yan siyasa, amma shugaban Buhari bai halarci bikin karshe da aka shirya a 2019 ba.
A makon nan ne Ayo Adebanjo ya ce wasan yaudara ake yi tsakanin Bola Tinubu da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce APC ba za ta ba Tinubu mulki ba
Sabon shugaban kungiyar Afenifere da ke kare hakki da muradun Yarbawa a kasar nan ya ce idan Bola Tinubu ya nemi tikitin APC a zaben 2023, ba zai dace ba.
Ayo Adebanjo ya ce Buhari ba zai ba Bola Tinubu mulki a 2023 ba, zai gwammace ya zabi Fulani.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng