Muna nan zuwa kanku, Shugaban sojin Najeriya ga Igboho da Dokubo
- Shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya, Laftanal janar Attahiru yace suna nan zuwa kan Sunday Igboho da Asari Dokubo
- Babban hafsin sojan yace babu shakka zasu yi iyakar kokarinsu wurin tabbatar da sun fattaki duk wani nau'in rashin tsaro
- Attahiru ya sha alwashin ganin bayan duk wasu masu tada kayar baya ko kungiyoyin assasa rashin tsaro
Rundunar sojin Najeriya nan kusa za ta koma farautar masu tada kayar baya kamar su Sunday Igboho da Asari Dokubo, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru yace.
Jan kunnen nan yana zuwa ne bayan da Attahiru ya halarci taron horar da kwamandojin soja na 2021.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, a cikin kwanakin nan ne Igboho ya bayyana cewa yankin kudu maso yamma baya daga cikin Najeriya.
Dokubo ya sanar da samar da gwamnatin gargajiya ta Biafra wacce ta hada da wasu sassan kudu maso gabas da kudu kudun kasar nan.
KU KARANTA: 2023: Dattawan arewa na zargin ana shiryawa yankin wata maƙarƙashiya
KU KARANTA: Ba za mu bada kunya ba, dukkan kallo ya dawo kanmu, Shugaban EFCC Bawa
Amma Attahiru yayi alkawarin cewa zai maganin duk wani kalubalen tsaro da ke addabar kasar nan, wanda ya hada da masu tada kayar baya irinsu Igboho da Dokubo.
"Rundunar sojin Najeriya karkashin shugabancina zata cigaba da zama a shirye tare da aiki da sauran jami'an tsaro wurin shawo kan matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.
"Rundunar karkashina za ta cigaba da zama a shirye wurin maganin kowanne mutum ko kungiya da take barazana ga zaman lafiya, tsaro da daidaito na kasar nan," ya sha alwashi.
A wani labari na daban, shugaban hukumar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen jihar Kano, Malam Isah Limita Muhammad yace hukumar ta bankado wata tafkekiyar gonar wiwi a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano.
Shugaban hukumar ya sanar da manema labarai hakan a jiya a garin Kano. Ya ce, "Yanzu muka bankado wata tafkekiyar gonar wiwi a Gwarzo kuma mun cafke mamallakinta. Za mu gurfanar dashi a gaban shari'a nan babu dadewa.
"Hakazalika, an sanar damu wata gonar a wani wuri na daban amma har yanzu bamu gano ta ba. Bayan mun kammala bincike za mu gurfanar da masu ita domin su fuskanci fushin shari'a."
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng