Ya samu kyautar N20K daga tsohon abokinsa da suka yi shekaru 6 suna zuwa makaranta kan alkhairin da yayi masa

Ya samu kyautar N20K daga tsohon abokinsa da suka yi shekaru 6 suna zuwa makaranta kan alkhairin da yayi masa

- Wani dan Najeriya, Nwoke Agulu, ya samu tukuici daga abokin karatun sa na makarantar sakandare kan yadda ya dunga taimaka masa zuwa makaranta

- Tsohon abokin nasa ya aika masa da kudi N20,000 domin nuna godiya a akan yadda ya sauƙaƙa rayuwarsa shekaru da yawa da suka gabata

- Mutane da yawa sun ce lallai mutumin aboki ne na kwarai tunda har ya iya tunawa da alkhairin da aka yi a shekarun baya

Wani dan Najeriya da aka ambata da suna Nwoke Agulu ya bayyana a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 22 ga Maris, yadda wani tsohon abokin karatunsa na makarantar sakandare yayi masa sha tara ta arziki.

Nwoke ya ce lokacin da abokin ya turo masa kudi N20,000 sai ya tambaye shi ko na menene, sai abokin karatun nasa ya bayyana cewa wannan tukuici ne kan yadda ya dunga daukarsa a kafarsa a bas din zuwa makaranta tsawon shekara shida.

KU KARANTA KUMA: Tukuicin sauya sheka:Omisore, Bankole, Dogara sun samu manyan mukamai a APC

Ya samu kyautar N20K daga tsohon abokinsa da suka yi shekaru 6 suna zuwa makaranta kan alkhairin da yayi masa
Ya samu kyautar N20K daga tsohon abokinsa da suka yi shekaru 6 suna zuwa makaranta kan alkhairin da yayi masa Hoto: @OkeyeCardinal
Asali: Twitter

Tuni mutane da dama suka yi sharhi a kan wallafar mutumin, suna masu cewa abokin karatun nasa mutum ne da ke nuna godiya ga aikin alkhairi.

Akwai wadanda suka yi wa mutumin addu’a a kan tunani irin nasa, suna rokon Allah ya albarkaci zuciyarsa mai cike da karamci.

KU KARANTA KUMA: Kada ‘yan Najeriya su sanya siyasa a harin da aka kai mun, in ji Ortom

Kalli wallafar mutumin a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da akayi a kan wallafar a kasa:

@CHIfreedom ya ce:

"Allah ya saka masa da alheri. Abokai irin sa ba su da yawa. Yaba kyauta zinare ne."

@thaddaeusdozie ya ce:

"Kuma nawa abokin ne ya saya min wayata ta farko a 2005, yana mai tuna min cewa na taba ba shi wando a shekarar 2001 yayin da muke makarantar sakandare."

@WorldFamousLuca ya ce:

"Taimakon mutane wani abu ne. Sannan wani abu ne na daban a garesu su tuna har ma su yaba."

@kamsilanky ya ce:

"Mutanen kirki suna tuna yadda aka taimaka musu yayin da suke kokarin zuwa sama. Allah ya albarkaci abokinka nagari."

A wani labari na daban, Fatima Amma Indimi, diyar biloniyan Maiduguri, ta je kafar sada zumunta inda tayi magana a kan yafiya, bayan shekaru da kanwarta ta aure tsohon saurayinta.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, Fatima Amma Indimi ta nuna tsabar rashin jin dadinta bayan kanwarta, Hauwa ta aure Mohammed Yar'Adua, dan marigayin manajan daraktan NNPC, Abubakar Yar'Adua.

Yayin da ake shirin auren, a bayyane Fatima ta nuna rashin amincewarta.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel