Yaron Hadimar Uwargidar Buhari ya saye dirkekeiyar mota mai kamar za ta yi magana
- Yaron hadimar uwargidar shugaban Najeriya ya nuna motar da ya saya
- Kingdibbo, ‘dan Dr. Hajo Sani, ya mallaki sabuwar marsandi a garejinsa
- Mahaifiyarsa, Hajo Sani, ta na cikin manyan mukarraban Aisha Buhari
Wani ‘dan mai ba uwargidar shugaban Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari, ya fito da hotunan wata mota mai tsada da ya mallaka.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wani yaron Dr. Hajo Sani, ya saye wata mota wanda za ace ‘son kowa, kuma kin wanda ya rasa.’
Wannan Bawan Allah mai amfani da sunan Kingdibbo a shafinsa na Instagram, shi ne ya wallafa hotunan sabuwar amaryar da ya yi.
Kingdibbo ya rubuta: “Baby Flex! #MyBaby Mercedes Benz # Alhamdulillah #AndMore.”
KU KARANTA: Matar Sanusi II ta yi Digirgir a fannin tattalin arziki a Jami’ar Ingila
Ma’ana dai ya yi amaryar mota kirar ‘Mercedes Benz’. Wannan attajiri ya kuma kara da godiya ga Allah madaukakin Sarki a shafin na sa.
Kingdibbo ba bakon fito da motocinsa a shafukan sada zumunta ba ne, ya kan nuna wa Duniya irin arzikin da Ubangiji ya yi masa.
Amma wannan sabuwar mota da ya mallaka mai tsada ce kwarai da gaske kamar yadda wadanda su ka san kan mota su ka bayyana mana.
Wannan mota kirar CLK, ko lamba ba a sa mata ba, da alamun ta kuma zo ne sabuwa a cikin ledarta.
KU KARANTA: Uwargidar Buhari ta baro Dubai, ta dawo Najeriya
Mahaifiyar Dibbo kamar yadda ake kiransa, Hajo Sani ta na cikin ‘yan gaban goshin Mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari, tun 2015.
Da farko an yi tunani gwamnatin nan ta Buhari ba za ta yi aiki da ofishin uwargidar shugaban kasa kamar yadda aka saba yi a Najeriya ba.
Kwanaki kun ji cewa 'Dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin Daura/Maiadua/Sandamu ya nuna hoton sabuwar gidan da ya gina a Abuja.
Hon. Fatuhu Mohammed wanda 'danuwa ne wurin mai girma Shugaban kasa Muhammad Buhari ya gina tanfatsetse gida a birnin tarayya.
Honarabul Mohammed ya ce ya gina wannan katafaren gidan na sa ne a cikin shekaru hudu.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng