Wata Ƙungiya ta ƙalubalanci Shugaba Buhari kan dukiyoyin da gwamnatinsa ke ƙwatowa

Wata Ƙungiya ta ƙalubalanci Shugaba Buhari kan dukiyoyin da gwamnatinsa ke ƙwatowa

- Wata Kungiya ta kalubalanci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan dukiyoyin da take kwatowa daga wadanda suka sace

- Kungiyar tace shugaba Buhari ya kasa cika alkawarin da ya daukar ma yan Najeriya cewa zai yaki cin hanci da rashawa

- Shugaban kungiyar ya yi ikirarin cewa ko da an kwato dukiyar to wasu daga cikin gwamnatin ke sama da fadi da ita

Wata Ƙungiya masu bada shawarwari kan harkokin mulki (CISLAC) ta ƙalubalanci gwamnatin shugaban ƙasa Buhari da rashin bayyana dukiyoyin da aka kwato.

KARANTA ANAN: Yaro dan shekara 13 ya burge mutane da dama a shafukan sada zumunta bayan ya kera abin hawa da kwalin sabulu

A cewar ƙungiyar, shekara shida kenan da hawa mulkin wannan gwamnatin amma babu wani abu da zaka iya nuna wa an kwato da suna yaƙi da cin hanci da rashawa da gwamnatin ke iƙirarin ta na yi.

CISLAC ta bayyana haka ne a wani taro da ta kira ranar Talata a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga 'yan majalisun ƙasar nan da su kafa dokar da zata bada damar ƙirƙirar hukumar kula da dokiyoyin da aka ƙwato.

KARANTA ANAN: Ya samu kyautar N20K daga tsohon abokinsa da suka yi shekaru 6 suna zuwa makaranta kan alkhairin da yayi masa

Shugaban CISLAC, Auwal Rafsanjani ya ƙara da cewa, duk da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi ma yan Najeriya alƙawarin zai fatattaki cin hanci da rashawa amma bai nuna sadaukarwa sosai ba wajen cika wannan alƙawarin.

Wata Ƙungiya ta ƙalubalanci Shugaba Buhari kan dukiyoyin da gwamnatinsa ke ƙwatowa
Wata Ƙungiya ta ƙalubalanci Shugaba Buhari kan dukiyoyin da gwamnatinsa ke ƙwatowa Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Auwal Rafsanjani ya yi iƙirarin cewa kuɗaɗe da dukiyoyin da shugaba Buhari ke ƙwatowa, wasu 'yan siyasa ke sace su a cikin gwamnatinsa.

A wani labarin kuma Gwamnatin Katsina ta bada umarnin buɗe makarantun kwana

Gwamnatin jihar Katsina ta bada umarnin buɗe makarantun kwanan dake faɗin jihar daga ranar Laraba 24 ga watan Maris, Sai dai gwamnatin tace duk daliban su koma makarantun dake kusa da garuruwan da suke zaune.

Ta kuma bada umarnin buɗe wasu makarantun guda biyar daga ranar 28 ga watan Maris.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Online view pixel