Bayan kanwarta tayi wuff da tsohon saurayinta, Fatima Indimi ta magantu kan yafiya

Bayan kanwarta tayi wuff da tsohon saurayinta, Fatima Indimi ta magantu kan yafiya

- Diyar hamshakin mai kudin Maiduguri, Fatima Indimi ta yi magana a kan yafiya a kafar sada zumunta

- Hakan ya biyo baya ne bayan shekaru uku da kanwarta ta aure tsohon saurayinta, Mohammed Yar'Adua

- Fatima Amma Indimi ta yi magana inda ta tunatar a kan mutuwa kuma tace ta yafe wa wasu da take tsammanin ba zata iya ba

Fatima Amma Indimi, diyar biloniyan Maiduguri, ta je kafar sada zumunta inda tayi magana a kan yafiya, bayan shekaru da kanwarta ta aure tsohon saurayinta.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, Fatima Amma Indimi ta nuna tsabar rashin jin dadinta bayan kanwarta, Hauwa ta aure Mohammed Yar'Adua, dan marigayin manajan daraktan NNPC, Abubakar Yar'Adua.

Yayin da ake shirin auren, a bayyane Fatima ta nuna rashin amincewarta.

KU KARANTA: Fani Kayode ya musanta cin zarafin ma'aikatansa na cikin gidansa, ya garzaya gaban kotu

Bayan kanwarta tayi wuff da tsohon saurayinta, Fatima Indimi ta magantu kan yafiya
Bayan kanwarta tayi wuff da tsohon saurayinta, Fatima Indimi ta magantu kan yafiya. Hoto daga @a.Indimi
Asali: Instagram

KU KARANTA: Alaka da ƴan bindiga: Matawalle ya rantse da Qur'ani, ya bukaci ƴan jiharsa da su yi hakan

"Wannan kwafsawa, tsohon saurayina ne saboda wani dalili kuma yanzu zaki dawo min dashi cikin rayuwata. A'a. Ba zan goyi bayan wannan ba. Akwai doka a wannan, a kakkabe 'yan uwa da abokan arzikin tsoffin masoya." Ta rubuta.

A ranar 21 ga watan Maris 2021, Fatima tayi wallafa a shafinta na Instagram a kan yafiya.

"Kun san, wurin karfe 3 na dare ina ta tunani. Mun san dukkanmu ba zaman har abada muka zo ba. Amma muna shirin tafiyar, ganin cewa bamu san lokacinta ba?" tace.

"Zaka ga cewa ka musgunawa wani da saninka ko babu saninka. Hakan kuwa ba tsakaninka bane da Ubangiji, tsakaninka ne da wannan mutumin. Na gano cewa ina son yin amfani da wannan damar wurin neman yafiya ga wadanda na taba a kowacce hanya.

"Akwai mutum daya da nake ganin kamar ba zan yafewa ba, amma daga karshe ina kokarin zama mutum tagari, na yafe muku duka. Alhamdulillah! Allah ya yi mana jagora zuwa hanya ta kwarai."

A wani labari na daban, sama da fasinjoji 100 da za su je Legas suka sha dogon zama a filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano a ranar Lahadi bayan jirgin sama na Aero Contractors ya yi saukar gaggawa bayan mintuna kadan da tashinsa.

Kamar yadda ɗaya daga cikin fasinjojin dake jirgin ya sanar, jirgin ya tashi ne da karfe 9:30 na safe bayan an fara jin wata ƙara daga injin ɗin dama na jirgin wanda kusan dukkan fasinjojin suka ji.

Ya ƙara da cewa, jim kadan matuƙin jirgin ya sanar dasu cewa zai koma inda ya taso saboda ƙarar da ake ji.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel