Jami'ar Yan Sanda da aka harba a rikicin zaɓen cike gurbi a Ekiti ta rasu

Jami'ar Yan Sanda da aka harba a rikicin zaɓen cike gurbi a Ekiti ta rasu

- Jami'ar yan sanda wacce aka harba ya yin tashin hankalin da ya faru ranar zaben maye gurbi a jihar Ekiti ta rigamu gidan gaskiya

- Gwamnan jihar Dr. Kayode Fayemi, ya bayyana a haka shafinsa na dandalin sada zumunta, twitter

Gwamnan ya siffata marigayiyar da jaruma, kuma mace mai kamar maza da ta yi zarra a aikin da maza sukafi yawa a cikinsa wato aikin dan sanda

Sajan Olawoye Bukola, jami'ar yan sanda da aka harba ya yin rikicin da ya ɓarke lokacin zaɓen cike gurbi a jihar Ekiti ta rasu, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi ne ya bayyanar da haka a shafinsa na dandalin sada zumunta, twitter, ya bayyana cewa jami'ar ta rasu da yammacin ranar Litinin.

KARANTA ANAN: 2023: Gwamnan jihar Edo ya fadi wanda ya kamata PDP ta tsaida a matsayin Shugaban kasa

Gwamnan ya kuma yima iyalan ta jaje da kuma rundunar 'yan sandan jihar bisa wannan babban rashi da suka yi.

Ya bayyana Bukola a matsayin mace mai kamar maza, kuma mai ƙima wacce tayi zarra a aikin da maza suka fi yawa wato aikin 'yan sanda.

"Ina mai matuƙar bakin cikin sanar muku da cewa sajan Bukola ta rasu, jami'ar 'yan sanda wacce aka harba lokacin rikicin zaɓen maye gurbi na mazaɓar Ekiti ta gabas mai lamba 1, ranar Asabar," inji Fayemi.

"Jami'ar ta yi jinya tun ranar da abun ya faru. Mun yi fatan da addu'ar cewa zata tashi, amma abun takaicin ta rasu da yammacin Litinin." .

"Marigayiyar sajan Olawoye ta kasance jaruma kuma mai ƙima wacce ta yi fice a aikin da maza suka fi yawa. Abun bakin ciki, ta rasa rayuwarta a lokacin da take aikinta."

KARANTA ANAN: Tukuicin sauya sheka:Omisore, Bankole, Dogara sun samu manyan mukamai a APC

"Tunani na da addu'a ta na tare da iyalan marigayiyar, musamman a wannan lokacin. Ina miƙa jaje na ga hukumar 'yan sanda kan wannan lamarin mai ban tausayi," Fayemi ya faɗa.

"An bani rahoton cewa mutanen da ake zargi an kaisu gaban kotu ranar Litinin. Gwamnatina zata tabbatar da an yi gaskiya akan wannan lamarin," a cewarsa.

Daga ƙarshe gwamnan yace: "Duk da banbancin jam'iyya da muke dashi, ya zama wajibi muyi aiki tare wajen kare tsarukan zaɓen mu kuma mu tseratar da rayuwar al'umma da dukiyoyinsu. Ina Addu'a Allah ya jikan ta."

A wani labarin kuma Gwamna Ganduje ya yi kira ga Maniyyata su zama Jakadun ƙasa nagari

Gwamnan ya yi wannna kira ne a ya yin da yake jawabi a wajen buɗe taron bita da ƙara wa juna sani da aka shiryawa mahajjatan bana, 2020/2021.

A cewarsa, yana fatan mahajjatan Kano su zama masu kyawawan ɗabi'u a ya yin gudanar da aikin su.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Online view pixel