2023: Gwamnan jihar Edo ya fadi wanda ya kamata PDP ta tsaida a matsayin Shugaban kasa

2023: Gwamnan jihar Edo ya fadi wanda ya kamata PDP ta tsaida a matsayin Shugaban kasa

- Maganar mulki ya koma yankin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya na kara karfi

- Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya na so ne a ba Kudu maso kudu tikiti a PDP

- Amma kungiyar Bala Mohammed Vanguard ta na kiran a ba Arewa maso gabas tuta

Daily Trust ta rahoto Gwamnan jihar Edo ya na kira ga jam’iyyarsu ta PDP ta fito da ‘dan takarar shugaban kasa daga shiyyar kudu maso kudancin Najeriya.

Godwin Obaseki ya yi jawabi ne a bikin da aka shriya domin karrama Dar Obih na zamansa mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar kudu maso kudu.

Da ya ke magana a wajen wannan taro, Obaseki ya ce adalci shi ne a bar mutumin kudu maso kudu ya zama shugaban kasa, kamar yadda aka yi a zaben 2011.

KU KARANTA: Na fada, na sake fada, Tinubu ba zai samu takara APC ba - Adebanjo

Obaseki ya ce “Dole kujerar shugban kasa ta dawo Kudu maso kudu, kuma kai (Orbih), dole ka zagaya kasar nan domin ka nuna masu ba za ka bari a zalunce mu ba.”

Mu na sa ran ka kawo takarar shugaban kasa zuwa yankin (Kudu maso kudu).” Inji Gwamnan.

Shi kuma shugaban kungiyar Bala Mohammed Vanguard (BAM-V), Kwamred Musa Haruna, ya yi kira ga jam’iyyar PDP ne ta tsaida mutumin Arewa maso gabas a 2023.

Da yake kaddamar da shugabannin kungiyar BAM-V, Musa Haruna ya ce Arewa maso gabas ne yankin da ya fi ci-baya, don haka ya kamata a ba su shuagaban kasa.

KU KARANTA: Obaseki zai fara binciken ‘barnar’ da Gwamnatin Oshiomhole ta yi

2023: Gwamnan jihar Edo ya fadi wanda ya kamata PDP ta tsaida a matsayin Shugaban kasa
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Amma kuma daya daga cikin manyan ‘yan APC na kasa, Ahmadu Haruna Danzago, ya na ganin duk abin da za ayi, a fito da ‘dan takarar shugaban kasan ne daga Kudu.

Kafin yanzu kun samu labarin cewa jam’iyyar PDP ta jihar Edo, ta ba uwar-jam’iyya shawara ta kai takarar shugaban kasa a zaben 2023 zuwa shiyyar Kudu maso kudun.

Shugaban PDP na Edo, Tony Aziegbemi ne ya yi wannan kira ne a lokacin da ya zanta da manema labarai a garin Benin, ya ce ya kamata yankin ya karasa cikon wa'adinsa.

Yankin kudu maso kudu sun samu mulki a karon farko ne a lokacin da Goodluck Jonathan ya dare kujerar shugaban kasa bayan rasuwar shugaba Umaru Musa Yar’adua.

A 2011 ne Goodluck Jonathan ya yi takara da kansa, ya kuma doke Muhammadu Buhari a CPC.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel