Jami'an Amotekun sun damke makiyaya 9 da shanu 100 a jihar Ondo

Jami'an Amotekun sun damke makiyaya 9 da shanu 100 a jihar Ondo

- Bayan wa'adin korar Fulani daga jihar, an kafa dokar hana kiwo a fili a Ondo

- Dokar ta haramta kiwo a fili, kiwo da dare, da kuma kiwo a kan manyan tituna

- Jami'ar hukumar Amotekun sun ce zasu sakesu idan suka yi alkawarin ba zasu sake ba

Hukumar tsaron kudu maso yammacin Najeriya, Amotekun, shiyar jihar Ondo ta damke shanu 100 da makiyaya kan laifin saba dokar hana kiwo a fili a jihar.

Jaridar TheCable ta rahoton kwamandan Amotekun na jihar, Adetunji Adeleye, da bayyana hakan.

A cewarsa, hukumar ta samu labarin yadda Shanu suka tare hanyar Ilesa-Akure.

Ya yi bayanin cewa sun tura jami'ai wajen inda suka damke makiyayan da dabbobinsu.

"Gwamnatin jihar ta samar da dokar hana kiwo a fili, kiwo da dare da kuma kiwo a kan titi. Mun samu labarin cewa Shanu sun tare titin Ilesa-Akure kuma sun shiga gonaki sun lalata. sai muka shiga muka damkesu," yace.

Yace sun kama dabbobin ne tare da masu kiwonsu.

KU KARANTA: Kar ka Jefa Najeria Cikin Yaƙi Kan Hijabi, Shugaban PFN ya Gargaɗi Gwamnan Kwara

Jami'an Amotekun sun dake makiyaya 9 da shanu 100 a jihar Ondo
Jami'an Amotekun sun dake makiyaya 9 da shanu 100 a jihar Ondo
Asali: Facebook

DUBA NAN: Sojoji za su yi luguden wuta na ‘mai uwa da wabe, za a kashe duk wanda ke cikin daji

Ya kara da cewa za'a sakesu muddin suka rattafa hannu kan takarda cewa ba zasu sake saba dokan hana kiwo a fili ba.

"An kamasu yanzu kuma ana tattaunawa da masu gonakin. Muddin suka yi alkawarin ba zasu sake lalata gonaki ba kuma zasu biya diyyar abinda suka lalata, zamu sake musu shanunsu," Adeleye ya kara.

A bangare guda, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa abokan aikinsa sun damu a dalilin harin da aka kai wa takwaransu, Samuel Ortom.

Jaridar This Day ta rahoto Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya na wannan bayani ne a ranar Litinin, 22 ga watan Maris, 2021, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya nuna cewa ya na sa rai kwanan nan za a kawo karshen matsalar rashin tsaron da ake fuskanta a bangarorin Najeriya.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel