Alaka da ƴan bindiga: Matawalle ya rantse da Qur'ani, ya bukaci ƴan jiharsa da su yi hakan

Alaka da ƴan bindiga: Matawalle ya rantse da Qur'ani, ya bukaci ƴan jiharsa da su yi hakan

- Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara ya rantse da Qur'ani kan cewa bashi da alaka kowacce iri da ƴan bindigar jiharsa

- Gwamnan ya kalubalanci dukkan masu fadi a ji da jami'an gwamnatinsa da su yi hakan in har basu da hannu a lamarin

- Ya sanar da jama'ar Zamfara cewa hakan ne kadai zai sa su iya gane masu assasa rashin tsaron da ya damu jihar

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi rantsuwa da Qur'ani kan cewa bashi da alaka da ƴan bindigan da ke addabar jiharsa.

Channels Tv ta ruwaito cewa, Ya kara da kalubalantar mazauna jihar, ba tare da duba matsayinsu ba, da su yi hakan domin tabbatar da cewa basu da hannu cikin rashin tsaro da ya addabi jihar.

Gwamnan ya yi hakan ne a ranar Lahadi a garin Gusau, babban birnin jihar yayin karbar lambar yabo da cibiyar karatun kur'ani ta Najeriya ta bashi a matsayin Khadimul Qur'an.

KU KARANTA: Bidiyon Amarya mai Adon Fuka-fukai ya Janyo Cece-kuce a Kafar Sada Zumunta

Ta'addanci: Matawalle yayi rantsuwa da Qur'ani, ya bukaci 'yan jiharsa da suyi hakan
Ta'addanci: Matawalle yayi rantsuwa da Qur'ani, ya bukaci 'yan jiharsa da suyi hakan. Hoto daga @Channelstv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hoton matashin bature sanye da kayan NYSC ya janyo cece-kuce

"Kamar yadda nake faɗi, lamarin rashin tsaron nan ba gwamnatin tarayya, gwamnoni ko jami'an tsaro kadai ya shafa ba. Lamarin rashin tsaro ya shafa kowa kuma kada mu siyasantar da lamarin.

“Na rantse da Qur'ani mai girma ban sani ba, bana daga ciki kuma bansan ko waye ke shirya hakan ba. Kada Allah ya bani abinda nake so a duniya idan na sani," yace.

Gwamnan Matawalle ya kara da cewa, "Ina kalubalantar jama'ar jihar Zamfara, daga Aliyu Gusau zuwa Yariman Bakura da sauran masu mukami a gwamnatina da su dauka rantsuwar nan."

Ya yi bayanin cewa, daga hakan ne mazauna jihar zasu gane wadanda ke ruruta wutar rashin tsaro da ke addabar jihar.

Gwamnan ya kwatanta halin tsaron jihar da yanzu da abun tsoro duk da kokarin da ake yi na dinke ɓarakar.

Ya jaddada cewa, a matsayinsa na babban jami'in tsaron Zamfara, zai yi duk abinda zai iya wurin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Gwamna Matawalle yace yana da amfani ga mazauna jihar su koma kasuwancinsu da sauran harkokinsu ba tare da tsoron za a cutar dasu ba.

Ya tabbatarwa jama'a cewa mulkinsa ya shirya tsaf kuma ya mayar da hankali wurin toshe rashin tsaron da ya addabi jihar dake yankin arewa maso yammacin ƙasar nan.

A wani labari na daban, Dino Melaye, tsohon sanatan da ya wakilci jihar Kogi ta yamma, yace babbar damfarar da ta taba faruwa a Afrika shine yadda aka goyawa Buhari baya ya samu shugabancin kasa a 2015.

Melaye ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a yayin da ya bayyana a wani shiri na gidan talabijin na Channels.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Melaye, wanda yanzu dan babbar jam'iyyar adawa ce ta PDP, ya bar jam'iyyar APC a shekarar 2018.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel