Yan bindigan da suka sace Sarkin Gargajiya A Jihar Ogun sun Buƙaci a basu 100 Miliyan

Yan bindigan da suka sace Sarkin Gargajiya A Jihar Ogun sun Buƙaci a basu 100 Miliyan

- Masu garkuwa da mutanen da suka kama sarkin gargajiya a jihar Ogun sun nemi iyalansa su biya 100 miliyan kafin su sake shi.

- Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunan ta tace da farko yan bindigan sun nemi a biya 200 miliyan amma bayan tattaunawa suka dawo 100 miliyan

- A kwanakin baya ne dai aka sace mutumin ya yin da yake kan hanyar sa ta koma wa gida bayan ya halarci wani taro.

Mutanen da sukayi garkuwa da wani shugaban al'umma a garin Imope dake ƙaramar hukumar Ijebu ta Arewa, Tajudeen Omotayo, sun buƙaci a biyasu 100 miliyan kuɗin fansa kafin su sake shi.

KARANTA ANAN: Kungiyar Arewa ga Ortom: Ka fito da hujjar da za ta nunawa Duniya Fulani sun kai maka hari

Yan bindigan da ba'a san ko suwaye ba sun yi awon gaba da Tajudeen Omotayo a ranar Asabar ɗin da ta gabata yayin da yake kan hanyarsa ta dawo wa daga wani taro da ya halarta.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an sace mutumin ne a hanyar sa ta dawo wa daga Ijebu-Ode a cikin motar sa mai lamaba W 3J9.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun ritsa shi ne a Oke-Eri, suka fiddo shi daga motarshi, suka tasa keyarsa zuwa wani wuri da ba'asan shi ba, aka bar motar da yake ciki anan wajen.

KARANTA ANAN: Rikicin Zaɓe: Da yuwuwar INEC ta soke wasu Jam'iyyu Saboda tayar da yamutsi

Sai dai wata majiya da ta buƙaci a sakaya sunanta daga garin Imope ta bayyana ma wakilin jaridar Punch ranar Litinin, ta bayyana cewa masu garkuwan sun nemi iyalan wanda suka sace da su biya 200 miliyan kuɗin fansa.

Majiyar ta ƙara da cewa bayan doguwar tattaunawa tsakanin su, mutanen sun rage kuɗin fansar zuwa 100 miliyan.

Waɗan da Suka Sace Wani Sarkin Gargajiya A Jihar Ogun Sun Buƙaci A Basu 100 Miliyan
Waɗan da Suka Sace Wani Sarkin Gargajiya A Jihar Ogun Sun Buƙaci A Basu 100 Miliyan Hoto: @Daily_trust
Asali: Twitter

Majiyar tace: "Waɗanda suka sace mutumin sun nemi iyalansa su biya 200 miliyan, amma zuwa yanzun sun ce a basu 100 miliyan."

A wani labarin kuma Ekiti ta bai wa makiyaya wa'adin makwanni 2 su yi rajista ko su tattara su bar jihar

Gwamnatin jihar Ekiti a Kudu maso gabashin Najeriya ta ba da wa'adin mako biyu ga makiyaya da manoma a fadin jihar cewa su yi rijista da gwamnatin jihar ko kuma su tattara nasu ya nasu su fita daga jihar baki ɗaya.

Tuni dokar ta fara aiki a yau Litinin 22 ga watan Maris, daga majiya mai tushe na jihar.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262