Ekiti ta bai wa makiyaya wa'adin makwanni 2 su yi rajista ko su tattara su bar jihar

Ekiti ta bai wa makiyaya wa'adin makwanni 2 su yi rajista ko su tattara su bar jihar

- Jihar Ekiti a kudanci ta baiwa makiyaya da manoma wa'adin makwanni 2 su yi rajista

- Jihar ta Ekiti ta kuma gargadesu da cewa kin yin hakan zai sa a fatattake su a fadin jihar

- Tuni dokar ta fara aiki a yau Litinin 22 ga watan Maris, daga majiya mai tushe na jihar

Gwamnatin jihar Ekiti a Kudu maso gabashin Najeriya ta ba da wa'adin mako biyu ga makiyaya da manoma a fadin jihar cewa su yi rijista da gwamnatin jihar ko kuma su tattara nasu ya nasu su fita daga jihar baki daya.

Tuni sanarwar ta bayyana wa'adin ya fara aiki tun ranar Lahadi, 22 ga watan Maris, BBC Hausa ta rahoto.

Cikin wata sanarwar kwamishinan aikin gona da wadatar abinci na jihar Dakta Olabode Adetoyi, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta lura cewa rikici tsakanin manoma da makiyaya na haifar da hadari ga lafiyar mutane da kuma kokarin wadata jihar da abinci.

Don haka daukar matakin rajistar ya zama wajibi ga gwamnati, don dakile matsalar rikici da ke ballewa tsakanin makiyayan da manoma.

KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya dage da addu'a, na hango rudani a nan gaba, in ji wani Fasto

Ekiti ta bai wa makiyaya wa'adin makwanni 2 su yirajista ko su tattara su bar jihar
Ekiti ta bai wa makiyaya wa'adin makwanni 2 su yirajista ko su tattara su bar jihar Hoto: hausa.leadership.ng
Asali: UGC

A baya cikin watan Fabrairun da ta gabata ne jihar ta nemi makiyayan da manoma da su yi rajistan na tsawon makwanni biyu, sai dai hukumomin jihar sun ce ba dukkaninsu ne suka yi rajistar ba.

Mai bada shawara na musamman ga Gwamnan jihar ta Ekiti Kayode Fayemi kan lamuran tsaro kuma shugaban kwamitin shiga tsakanin makiyaya da manoma a jihar Birgediya-Janar Ebenezer Ogundana mai ritaya., ya yi gargadi a cikin sanarwar, yana mai cewa

''Za a kori duk wanda ya ki yin wannan rajista daga jihar''

Jihar Ekiti na daya daga cikin jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya da suka yi kokarin haramta kiwo barkatai a yankunansu.

KU KARANTA: 'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojojin Kamaru a Najeriya

A wani labarin, Wata kungiyar Fulani da ke ikirarin kare muradin Fulanin (FUNAM), ta ce ita ke da alhakin yunkurin kashe Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, PM News ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa da aka bai wa manema labarai, wanda aka yi kuskuren rubuta sunan Ortom sau da yawa, kungiyar ta ce manufarta ita ce kashe Ortom.

Ta sha alwashin hallaka Ortom, saboda kamar yadda ta yi ikirarin, yana adawa da Fulani.

"Mayakanmu sun kai wannan harin na tarihi don aika babban sako ga Ortum da wadanda suka hada kai dashi", kungiyar ta yi ikirarin a wata sanarwa da Umar Amir Shehu ya sanya hannu.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel