Rikicin Zaɓe: Da yuwuwar INEC ta soke wasu Jam'iyyu Saboda tayar da yamutsi

Rikicin Zaɓe: Da yuwuwar INEC ta soke wasu Jam'iyyu Saboda tayar da yamutsi

- Wata ƙungiyar cigaban demokaraɗiyya a yammacin Africa (CDD) ta kirayi hukumar zaɓe da ta dau tsattsauran mataki akan duk wanda aka kama da tada yamutsi yayin gudanar da zaɓe

- Shugabar hukumar ce ta bayyana haka yayin da take jawabi kan abinda ya faru a jihar Ekiti

- Hukunar ta kuma yi kira ga 'yan majalisun ƙasar nan da su yi amfani da damar su su gudanar da gyaran kundin tsarin zaɓen ƙasar nan

Wata ƙungiyar cigaban demokaraɗiyya (CDD) ta kirayi hukumar zaɓe ta ƙasar nan INEC da ta ɗauki tsattsauran mataki na soke duk jam'iyyun da suke da hannu wajen tayar da rikici a ya yin gudanar da zaɓe.

KARANTA ANAN: Kungiyar Gwamnoni (NGF) Ta Bayyana Matakin Da Zata Ɗauka Kan Harin Da Aka Kaima Gwamnan Benue

Ƙingiyar tace duk wani ɗan takara ko jam'iyya da aka kama da hannu wajen tayar da rikici yayin zaɓe to kamata ya yi INEC ta ɗauki tsattsauran mataki akansa koma ta soke jam'iyyar kwata-kwata.

Ya yin da CDD ke kira ga ɗaukar mataki ga waɗan da suka karya dokar zaɓe, ƙungiyar ta ce akwai babbar buƙatar a sake gyara kundin tsarin zaɓen.

Shugaban CDD, Idayat Hassan, ta bayyana haka a wani jawabi da ta fitar, kuma ta nuna takaicinta kan rikicin da ya faru a ya yin gudanar da zaɓen cike gurbi a jihar Ekiti wanda ya yi sanadiyyar dakatar da zaɓen.

Shugabar tace: "Muna ta'aziyya ga dukkan iyalan waɗan da aka kashe a rumfar zaɓe mai lamba 007, gunduma mai lamba 07, kuma muna kira ga shuwagabanni da kada abar mutuwar su ta tafi haka kawai."

"Kuma muna kira ga rundunar 'yan sanda da ta gaggauta kamo waɗan da keda hannu kan kisan masu zaɓe uku, da yar sandan da aka jikkata, da kuma ma'aikacin INEC don su fuskanci hukunci dai-dai da abinda suka aikata." a cewarta.

KARANTA ANAN: 'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojojin Kamaru a Najeriya

"Kamar yadda muke fuskantar babban zaɓen 2023, ya kamata INEC ta shirya ɗaukar tsatsauran mataki kan duk wani ɗan takara ko wata jam'iyya da aka samu da hannu wajen tada yamutsi a lokacin zaɓe. Muna fatan babban zaɓen dake tafe na 2023 zai gudana cikin kwanciyar hankali." inji shugaban CDD.

"Duk da yarjejiniyar da akayi da 'yan takara don gudanar da sahihin zaɓe a ranar 17 ga watan Maris, amma wasu ɓata gari sun zo sun ɓata shirin gaba ɗaya." injita.

Rikicin Zaɓe: Da yuwuwar INEC ta soke wasu Jam'iyyu Saboda tayar da yamutsi
Rikicin Zaɓe: Da yuwuwar INEC ta soke wasu Jam'iyyu Saboda tayar da yamutsi Hoto: @Inecnigeria
Asali: Twitter

Ta kuma ƙara da cewa: "Kamar yadda muke shirye-shiryen gudanar da zaɓe a jihar Anambra 2021, Ekiti da Osun 2022, ya kamata majalisun ƙasar nan suyi amfani da damar da kundin tsarin mulkin da ƙasar nan ya basu, su gyara dokokin zaɓe, su kafa hukumar da zata sa ido kan laifuffukan zaɓe. Hukumar zata bincika kuma ta hukunta duk wanda aka kama da laifi."

A wani labarin kuma Burutai da sauran hafsoshin tsaro za su bayyana a gaban majalisa kan batun kudin makamai

Kwamitin gaggawa da aka kafa domin binciken kudaden sayen makamai da amfani da su na Majalisar Wakilan Najeriya ya gayyaci hafsoshin tsaro da sauran shugabannin tsaron kasar.

Gayyatar ta biyo bayan kalaman mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro a makon jiya.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262