Zanga Zanga: Iyayen Daliban Da Aka Sace A Kaduna Sun Bijirewa Umarnin Sojoji

Zanga Zanga: Iyayen Daliban Da Aka Sace A Kaduna Sun Bijirewa Umarnin Sojoji

- Iyayen ragowar ɗaliban da aka sace a makarantar koyon ilimin gandun daji dake Afaka, jihar kaduna sun cigaba da zanga-zanga.

- Iyayen sun fara zanga-zangar ran Alhamis ɗin satin daya gabata kuma sunce yau ba inda zasu sai an tabbatar musu da za'a kuɓutar da 'yaƴansu.

- Sun kuma bayyanar da cewa tun bayan sace yayan su basu sake jin wani labari daga gwamnati ba

Iyayen ɗalibai 39 da aka sace a makarantar koyon ilimin gandun daji (FCFM) mallakar gwamnatin tarayya dake Afaka, jihar Kaduna sun cigaba da zanga-zangar neman a kuɓutar musu da 'yayansu.

KARANTA ANAN: A karkashin mulkin Tinubu ne kadai Najeriya za ta daidaita, in ji wasu manyan arewa

Cigaba da gudanar da zanga-zangar na nuna cewa sun bijirewa umarnin sojoji da suka basu na su zauna a gidajensu, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Iyayen, waɗan da sun yi zanga-zangar ran Alhamis ɗin satin da ya gabata sun ce ba zasu koma gida ba yau har sai gwamnati ta tabbatar musu zata kuɓutar da 'yayan su.

Ana zanga-zangar ne a cikin harabar makarantar FCFM ɗake hanyar filin jirgin sama a jihar Kaduna.

Zanga Zanga: Iyayen Daliban Da Aka Sace A Kaduna Sun Bijirewa Umarnin Sojoji
Zanga Zanga: Iyayen Daliban Da Aka Sace A Kaduna Sun Bijirewa Umarnin Sojoji Hoto: @Daily_trust
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Kungiyar Arewa ga Ortom: Ka fito da hujjar da za ta nunawa Duniya Fulani sun kai maka hari

Masu zanga-zangar na ɗauke da hotunan yaran su da aka sace da kuma kati ɗauke da rubutun 'A kuɓutar da 'yayan mu'.

Iyayen ɗaliban sun koka cewa tun sanda aka ɗauke 'ya'yansu har yanzun basu ji wani labari daga gwamnati ko hukumar makaranta kan ƙoƙarin da ake don ganin an kuɓutar da 'yayan nasu ba.

A wani labarin kuma Ku Cigaba Da Hakuri Da Gwamnatin Buhari, APC, Minista Ya Roƙi Yan Najeria

Ministan ayyuka na musamman, Senator George Akume, ya yi kira ga yan Najeriya su ƙara hakuri da gwamnatin shugaba Buhari

A cewar ministan, gwamnatin APC na da kudirori da shirye- shirye masu kyau da suka tanadar wa 'yan Najeriya.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262