Ku Cigaba Da Hakuri Da Gwamnatin Buhari, APC, Minista Ya Roƙi Yan Najeria
- Ministan ayyuka na musamman, Senator George Akume, ya yi kira ga yan Najeriya su ƙara hakuri da gwamnatin shugaba Buhari
- A cewar ministan, gwamnatin APC na da kudirori da shirye-shirye masu kyau da suka tanadar wa 'yan Najeriya
- Ministan ya yi wannnan jawabi ne a ya yin taron ƙarɓar wani jigo a jihar Benue zuwa jam'iyyar APC
Ministan ayyuka na musamman da kuma wasu al'amuran gwamnati, Senator George Akume, ya kirayi 'yan Najeriya da su cigaba da hakuri da gwamnatin APC.
KARANTA ANAN: Buhari Ya Yi Martani Kan Harin Da Ƴan Bindiga Suka Kaiwa Ortom
Akume ya yi wannan kira ne a ƙarshen mako bayan wani shahararren ɗan kasuwa, Moses Ayom, ya yi rijistar zama cikakken ɗan APC a garin Ihugh, ƙaramar hukumar Vandekiya a jihar Benue.
Akume, wanda tsohon gwamnan jihar Benue ne, yakasance babban baƙo na musamman a taron karɓar Ayom zuwa jam'iyyar APC, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ministan ya ce ya kamata 'yan Najeriya su ƙara hakuri da yarda da gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yinda suke amfanuwa daga kudirorinsa da tsare-tsarensa.
KARANTA ANAN: Ya kamata Buhari ya dage da addu'a, na hango rudani a nan gaba, in ji wani Fasto
Ministan ya bayyana Ayom a matsayin wani ginshiƙi a fannin kasuwanci da kuma Siyasa, ya kuma ƙara da cewa shigar sa APC ya ƙarawa jam'iyyar ɗaukaka a jihar.
Anashi ɓangaren Ayum ya bayyyana cewa:
"Duk da matsalar karyewar tattalin arziƙi da karancin albarkatun kasa ga kuma matsalar rashin tsaro da APC ta tsinci kanta a ciki, amma jam'iyyar ta nuna ƙwarewarta kuma ta nuna cewa jam'iyyar al'ummace. Ina farin cikin kasancewa ɗaya daga cikin ƴaƴan APC, jam'iyyar da mutane masu basira kuma abun kwaikwayo ke jagorantarta."
A wani labarin kuma SERAP Ta Kai Ƙarar Ahmad Lawan Da Gbajabiamila Kan Ɓatar Biliyan 4.4 na Kuɗin Majalisa
Ƙungiyar dake fafutukar kare haƙƙin bil'adama ta SERAP ta shigar da ƙarar kakakin majaƙisar wakilai da kuma shugaban majalisar dattawa kan ɓatan wasu kuɗaɗen da aka ware ma majalisa
SERAP ta shigar da ƙarar ne biyo bayan wallafa rahoton ɓatar kuɗin da ofishin dake sa ido kan al'amuran kuɗi (Auditor General) na ƙasar nan ya fitar.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .
Asali: Legit.ng