Da Sauran Kwana: FRSC Ta Ceci Wasu Fasinjoji Daga Hannun Bugaggen Direba

Da Sauran Kwana: FRSC Ta Ceci Wasu Fasinjoji Daga Hannun Bugaggen Direba

- Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa FRSC ta ce ta ceci wasu fasinjoji daga hannun wani direba da yasha giya kafin ya fara tuƙi.

- FRSC ta ce ta samu kiran gaggawa daga ɗaya daga cikin fasinjojin cikin motar kan irin tuƙin da direban ke musu, inda ba tare da ɓata lokaci ba hukunar ta umarci jami'anta su kama motar

- Bayan kama direban an kai shi asibiti aka yi masa gwaji don tabbatar da abun da fasinjan suka faɗa kuma angano Gaskiya ne

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa tace ta ɗauki matakin gaggawa bayan wani kira da wasu fasinjoji sukai mata cewa su taimaka su kuɓutar dasu daga hannun direban da ya ɗakko su don yana gudun wuce ƙima wanda ka iya jawo mummunan haɗari.

KARANTA ANAN: APC ba zata shiga zaɓen ƙananan hukumomi ba a Jihar Sokoto

Mai magana da yawun hukumar Bisi Kazeem ya bayyana cewa:

"An damƙe bugaggen direban da misalin ƙarfe 1:35 na yamma a kyakyama, ƙaramar hukumar Ogere dake jihar Ogun bayan fasinjojin motar sun kira kwamandan yankin sun shaida masa yana yin yadda direban ke tuƙa su."

"Ɗaya daga cikin fasinjan motar, Mrs Matina, ta bayyana cewa jin kaɗan da fara tafiyarsu suka fahimci direban na tuƙi ne da ƙarfin giyar daya sha wanda yasa fasinjan suka ƙalubalance shi akan hakan. Ta kara da cewa direban yaƙi jin gargaɗin da suka masa, daga nan suka ɗauki matakin kiran FRSC dan su kuɓutar da su." injishi.

Da Sauran Kwana: FRSC Ta CecI Wasu Fasinjoji Daga Hannun Bugaggen Direba
Da Sauran Kwana: FRSC Ta CecI Wasu Fasinjoji Daga Hannun Bugaggen Direba Hoto: @FRSCNigeria
Source: Twitter

Kazeem ya ce, bayan kwamandan yankin ya samu rahoton, nan take ya ba jami'ansa umarnin fita sintiri don su kamo wannan direban kuma su tabbatar da sun kamo motar wacce aka bayyana ta da 'farar mota Bas ƙirar Toyota' mai lamabar rijista FKJ 991 YA.

KARANTA ANAN: Wata sabuwa: Tsagerun Neja-Delta su na neman su fatattaki kamfanonin da ke aikin hako fetur

Bayan sun kama motar da direban, jami'an sun kai direban anyi masa gwajin shaye-shaye, sakamakon ya nuna 0.18 wanda ya zarta hakali sosai, ya kuma zarta dokar tuƙi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa shugaban jami'an da suka jagoranci kuɓutar da fasinjojin ya nuna farin cikin sa ga nasarar kuɓutar da su.

Ya kuma yi kira ga direbobi da su rinƙa kula da sauraron fasinjan su, yana mai cewa sauka lafiya muradin kowa ne.

A wani labarin kuma Dole in binciki satar N30bn a kwangilar ruwan da Oshiomhole su ka yi inji Gwamna Obaseki

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yi magana game da matakin da ya dauka na binciken aikin gwamnatin da ta shude ta Adams Oshiomhole.

Obaseki ya ce kwangilolin da Oshiomhole ya bada da yake ofis, sun fi na yanzu tsada.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Source: Legit.ng

Online view pixel