Buhari Ya Yi Martani Kan Harin Da Ƴan Bindiga Suka Kaiwa Ortom
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da yan bindiga suka kai wa Gwamna Samuel Ortom
- Shugaban kasar ya kuma gargadi yan siyasa su dena amfani da harin domin cimma manufofinsu na siyasa
- Shugaba Buhari ya kuma bukaci masu bincike da rundunar yan sanda ta aike Benue su binciko wadanda ke da hannu a hukunta su
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi martani kan harin da yan bindiga suka kai wa Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, inda ya gargadi yan siyasa su dena amfani da harin don cimma burinsu na siyasa.
Yan bindiga sun bude wa tawagar gwamnan wuta a lokacin da ya ke dawowa daga gonarsa a ranar Asabar.
DUBA WANNAN: Jam'iyyar APC Ta Kusa Rushewa, In Ji Gwamna Aminu Tambuwal
Mutane da dama sunyi martani game da harin inda suka yi kira ga gwamnatin tarayya ta magance kallubalen tsaro da ke adabar sassa da dama na kasar.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta soki shugaban kasar saboda jinkirin da ya yi na martani kan harin.
Amma cikin sanarwar da ya fitar a daren Lahadi, shugaban kasar ta bakin kakakinsa Garba Shehu ya yi tir da harin inda ya bukaci hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike.
KU KARANTA: Mummunan Gobara Ta Laƙume Shaguna 63 a Kasuwar Jihar Zamfara
"Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tir da harin da aka kaiwa Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, inda ya ce ba za a amince da muggan hare-haren da ake kai wa mutane a garin ba ciki har da wanda aka kai wa gwamnan a baya bayan nan.
"Shugaban kasar ya yi maraba da masu bincike da aike daga hedkwatan yan sanda ta Abuja inda ya bukaci su binciko duk wanda ke da hannu su gurfanar da su.
"Shugaba Buhari ya ce bai dace a siyasantar da lamarin mara dadi ba inda ya ce duk abinda ya samu wani dan Nigeria tamkar kasar baki daya abin ya shafa," wani sashi na sanarwar da Garba Shehu ya fitar a madadin Shugaban Kasa.
A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.
Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.
Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng