SERAP Ta Kai Ƙarar Ahmad Lawan Da Gbajabiamila Kan Ɓatar Biliyan 4.4 na Kuɗin Majalisa

SERAP Ta Kai Ƙarar Ahmad Lawan Da Gbajabiamila Kan Ɓatar Biliyan 4.4 na Kuɗin Majalisa

- Ƙungiyar dake fafutukar kare haƙƙin bil'adama ta SERAP ta shigar da ƙarar kakakin majaƙisar wakilai da kuma shugaban majalisar dattawa kan ɓatan wasu kuɗaɗen da aka ware ma majalisa

- SERAP ta shigar da ƙarar ne biyo bayan wallafa rahoton ɓatar kuɗin da ofishin dake sa ido kan al'amuran kuɗi (Auditor General) na ƙasar nan ya fitar

- Ofishin babban oditan ƙasa ya fitar da rahoton batar kuɗaɗe da suka kai 4.4 biliyan a cikin rahotonsa na shekarar 2015, 2017, da 2018.

Ƙungiyar dake fafutukar kare hakkin bil'adama ta SERAP ta shigar da karar shugaban majalisar dattijai , Dr Ahmad Lawan, da shugaban majalisar wakilai, Mr Femi Gbajabiamila, bisa zargin batar da naira N4.4bn na kudin da aka ware ma majalisa.

KARANTA ANAN: Za a yiwa malaman addini alluran rigakafin Korona saboda su jawo hankalin mabiyansu

SERAP ta bayyana cewa zargin batar kudin ya samo asali a cikin rahotanni uku na shekara-shekara da ofishin oditan ƙasar nan ya fitar, Punch ta ruwaito.

Karar ta biyo bayan wallafa bayanan shekarar 2015, 2017 da 2018 inda babban ofishin dake sa ido na kasar nan ya fitar.

Rahoton ya nuna damuwa kan yadda aka karkatar hadi da salwantar da dukiyar ƙasa, da kuma neman dawowa da dukkanin wasu kudi da suka salwanta, sannan ya nemi duk wata shaidar dawo da kudin da suka salwanta an kawo ta ofishinsa.

A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/366/2021 wadda aka shigar a babbar kotu a Abuja ranar Jumaa da ta wuce, SERAP ta nemi dokar da zata sanya Dr Lawan, da Mr Gbajabiamila dole suyi aikin da kundin mulki ya tanadar musu domin tabbatar sahihin bincike akan zargin cewa biliyan N4.4 da aka ware majalisar kasa sun ɓace.

SERAP Ta Kai Ƙarar Ahmad Lawan Da Gbajabiamila Kan Ɓatar Biliyan 4.4 Kuɗin Majalisa
SERAP Ta Kai Ƙarar Ahmad Lawan Da Gbajabiamila Kan Ɓatar Biliyan 4.4 Kuɗin Majalisa Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

A cikin karar SERAP ta kafa hujja da cewa:

"Kundin tsarin mulkin kasa na 1999, wanda ya ba majalisar kasa hurumin yaki da cin hanci da kuma tabbatar gaskiya wajen gudanarwa da amfani da dukiyar kasa."

KARANTA ANAN: Kungiyar Gwamnoni (NGF) Ta Bayyana Matakin Da Zata Ɗauka Kan Harin Da Aka Kaima Gwamnan Benue

"Sahihanci da gaskiya wajen gudanar da dukiyar al'umma suna da matukar muhimmanci wajen samar da cigaba, jindadin al'umma da walwala, da kuma tafiyar da lamuran mulki da bin tsarin doka"

"Majalisar kasa tana da hurumin tabbatar da cewa zarge-zargen cin hanci da rashin gundanarwa yadda yakamata da ofishin babban oditan kasa ya bayyana an bincike su yadda ya dace cikin gaggawa da kuma sahihanci"

"Gazawar majalisa wajen bincike yadda yakamata da kuma tura sakamakon zuwa ga hukumomin yaki da cin hanci a kan zarge-zargen da aka kawo a cikin rahoton shekara shekara na shekarun 2015, 2017, 2018, hakan saba ma sashi na 4, 88 da 89 na alhakin kula hakkokin al'umma da doka ta tanadar ma majalisun a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya"

A wani labarin kuma Wasu 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Sarkin Gargajiya A Ogun

Wani nakusa da wanda aka sace yace mutanen sun farmaki Omotayo ne kan hanyarsa ta komawa gida

Rundunar 'yan sandan jihar Ogun sun tabbatar da faruwar lamarin sai dai basu bada cikakken bayani ba domin suna kan bincike

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Source: Legit.ng

Online view pixel