Kungiyar Gwamnoni (NGF) Ta Bayyana Matakin Da Zata Ɗauka Kan Harin Da Aka Kaima Gwamnan Benue
- Kungiyar gwamnonin kasar nan ta bayyana cewa ba zata zura ido tana kallo ana kaima 'yayanta hari don ganin bayan su ba
- Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayede Fayemi, ya ce zasu gudanar da tsattsauran bincike don gano wadan da suka kaima gwamnan Benue hari
- Ya yi kira ga gwamnonin da su tsaya tsayin daka don kare al'ummar da suke shugabanta ba tare da jin tsoron wasu bata gari ba.
Ƙungiyar gwamnonin ƙasar nan (NGF) ta ce harin da aka kaima gwamnan jihar Benue, Dr. Samuel Ortom, don a rabashi da rayuwarsa ya yi matuƙar girgiza su kuma dole su farka daga baccin da suke yi.
A wani jawabi da ƙungiyar ta fitar ranar lahadi ta jajantawa gwamnan da kuma al'ummar jihar ta Benue kan wannan labari mara daɗi da ya faru da gwamnan su.
KARANTA ANAN: 2023: Ba zan goyi bayan Jonathan ba idan ya tsaya takara a APC, in ji Wike
Shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, ya yi Allah wadai da lamarin gaba ɗayan sa, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
A jawabin shugaban, a madadin sauran gwamnonin, ya bayyana cewa zasu zakulo duk wanda yake da hannu akan wannan harin.
"NGF na tabbatar da cewa bazasu amince da duk wani yunƙuri na ganin bayan gwamnan jihar Benue ba, kuma baza su taɓa samun nasara akanshi ba." a cewar shugaban NGF.
"Kwanan nan a ka tsinci gawar ɗan uwan ɗaya daga cikin tsofaffin gwamnonin jihar cikin jini. Wannan mummunan aikin na gayyato tashin hankali ne a jihar, kuma wannan yunƙurin na kashe 'yan jihar bazai ɗore ba," Inji Fayemi.
KARANTA ANAN: Muna cikin hali mai wuya, makiyaya 30 da shanu 322 sun bace a Anambra: Kungiyar Miyetti Allah
Ya ƙara da cewa: "Ƙungiyar gwamnoni zata cigaba da ƙarfafa ma gwamnonin ƙasar nan 36 guiwa su tsaya tsayin daka wajen kare al'ummar da suke jagoranta ba tare jin tsoron wasu waɗan da basa ma Najeriya fatan alkairi ba."
"Baza mu bar duk wani aikin ta'addanci ba, bawai a jihar Benue kaɗai ba, a koma ina ne a faɗin ƙasar nan," a cewarsa.
Shugaban gwamnonin ya ƙara da cewa bayan addu'a da fatan alkhairi da suke ma gwamna Ortom, za kuma su maida hankali wajen ganin anbi sawun waɗanda suka kai masa harin, a kamo su kuma a hukunta su dai-dai da abinda suka aikata.
Daga ƙarshe, Fayemi ya yi addu'a ga gwamnan Benue da kuma yi masa fatan dogowar rayuwa nan gaba.
A wani labarin kuma Za a yiwa malaman addini alluran rigakafin Korona saboda su jawo hankalin mabiyansu
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, zata hada hannu da malamai wajen gudanar allurar Korona.
Tuni Sarkin Musulmi ya bai wa malamai umarnin su koma garuruwansu don wayarwa mutane kai.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .
Asali: Legit.ng