Wasu 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Sarkin Gargajiya A Ogun

Wasu 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Sarkin Gargajiya A Ogun

- Wasu 'yan bindiga da ba'a gane ko suwaye ba sun farmaki wani sarkin gargajiya a jihar Ogun yayin da yake dawo wa daga zuwa biyan buƙata.

- Wani nakusa da wanda aka sace yace mutanen sun farmaki Omotayo ne kan hanyarsa ta komawa gida

- Rundunar 'yan sandan jihar Ogun sun tabbatar da faruwar lamarin sai dai basu bada cikakken bayani ba domin suna kan bincike

Wasu 'yan bindiga da ba'a gano ko suwaye ba har yanzun, sun farmaki magajin garin Imope Ijebu dake karamar hukumar Ijebu ta arewa mai suna, Chief Kolawole Omotayo, kuma suka yi awon gaba da shi.

KARANTA ANAN: Bayan yin rigakafin Korona da kwana 2, Firaminista ya kamu da Korona

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, an sace Omotayo ne akan hanyar Oke Eri-Imope, yana kan hanyarsa ta komawa gida daga Ijebu-Ode, inda yaje domin siyo wani abu.

Wani na kusa da magajin garin ya faɗa ma manema labarai cewa 'yan bindigar sun harbi tayoyin motar da yake ciki guda biyu, wanda take da lambar rijista 'WJ9'.

Wasu 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Sarkin Gargajiya A Ogun
Wasu 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Sarkin Gargajiya A Ogun Hoto: @Daily_trust
Asali: Twitter

Sun kuma fasa injin motar da harsashi, wanda hakan ya basu dama suka cimmasa suka fito dashi daga cikin motar kuma suka tasa shi zuwa cikin daji.

KARANTA ANAN: Albishir matasa: Shugaba Buhari zai fara tallafawa matasa don rage radadin Korona

Jami'i mai magana da yawun 'yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Oyeyemi, ya ce ba zai iya bada bayanin yadda lamarin ya faru ba amma ya tabbatar da cewa rundunar 'yan sanda na gunadar da bincike a kan lamarin.

Rahoto ya bayyana cewa mutumin da aka sace shine shugaban inyamurai na garin Ijebu.

A wani labarin kuma Gwamnati ta ce ba za ta tilastawa 'yan Najeriya yin rigakafin Korona ba

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta roka, maimakon tilasta wa kowa ya yi allurar rigakafin Korona ta Oxford AstraZeneca, a cewar Olorunnibe Mamora, Karamin Ministan Lafiya.

A cewarsa, gwamnati za ta bi hanyar wayar da kai ne domin mutane su aminta da allurar.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Online view pixel