Tallafin Korona: CBN ya ninka Kuɗaɗen da za'a tallafawa magidanta da masu ƙananan sana'o'i
- CBN ya ninka kuɗin da aka ware ma shirin bada rance ga magidanta da masu ƙananan sana'o'i wato (TCF) daga 150 biliyan zuwa 300 Biliyan.
- Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bayyana haka yayin duɗe taron ƙara ma juna sani karo na 30 da ake yiwa masu kula da sha'anin kuɗi
- A kwanan nan dai, an sake buɗe shafin yanar gizo a karo na biyu ga 'yan Najeriya domin neman rancen a tsarin na TCF
Babban bankin Najeriya (CBN) ya ninka kuɗaɗen da aka ware don tallafawa magidanta da masu ƙananan sana'o'i (TCF) daga 150 biliyan zuws 300 Biliyan.
Tsarin na TCF wanda aka sake buɗewa kwanan nan na bada rancen kuɗi ga magidanta da masu ƙananan san'o'i waɗan da annobar korona ta shafa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Bayan yin rigakafin Korona da kwana 2, Firaminista ya kamu da Korona
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana haka yayin buɗe taron ƙarama juna sani karo na 30 da bankin ke shirya ma masu kula da sha'anin kuɗi wanda ya gudana ta fasahar zamani (Virtually).
Gwaman wanda mataimakinsa akan ayyukan kamfanoni, Adamu Lamtek, ya wakilta yace ya zuwa yanzun an rabar da kuɗaɗe N149.21 biliyan ga mutane 316,869, saboda haka ne ma aka ninka kuɗin don 'yan Najeriya da dama su amfani da shirin.
A cewarsa wannan shirin da gwamnati ta ɓullo dashi zai ƙara yawan hada-hadar kuɗi a cikin ƙasa wanda hakan ka iya haɓɓaka tattalin arziƙin Najeriya.

Asali: Twitter
KARANTA ANAN: Da duminsa: INEC ta dakatar da zaben maye gurbi na Ekiti saboda zubda jini
Ya ce: "An yanke wannan hukunci ne saboda karuwar mutane da suke bukata, kuma wannan shiri ana cike shi ne ta yanar gizo, baya ɗaukar wani lokaci wajen cikewa."
Ya yin da yake martani kan maganganun ɗake yawo cewa CBN ya canza matsayarsa akan hada-hadar kuɗin yanar gizo 'Cryptocurrency' Gwamnan yace: "CBN bata bada wata sabuwar doka akan kuɗin ba, kowa yasan matsayar mu akan kasuwancin, kuma bamu canza ba."
A wani labarin kuma Shugaban NDLEA, Marwa ya ce ta'ammali da miyagun kwayoyi ya fi kamari a Kudu maso Yamma
Buba Marwa, shugaban hukumar hana fatauci da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ya bayyana cewa a yanzuhaka yankin Kudu maso Yammacin Najeriya ya na cikinwadanda suka fi shan miyagun kwayoyi a kasar.
Shugaban na NDLEA ya samar da kididdiga game da yawan ta’ammali miyagun kwayoyi a yankuna da dama na Najeriya.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .
Asali: Legit.ng