Da duminsa: INEC ta dakatar da zaben maye gurbi na Ekiti saboda zubda jini

Da duminsa: INEC ta dakatar da zaben maye gurbi na Ekiti saboda zubda jini

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta dakatar da zaben maye gurbi a jihar Ekiti

- Hukumar tace hakan ya biyo bayan mutuwar masu kada kuri'a uku, da kuma jigatar wasu ma'aikata da jami'an tsaro

- A yau Asabar ne ake zaben maye gurbin kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ekiti ta gabas

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta dakatar da zaben maye gurbin kujerar mazabar Ekiti ta gabas, jihar Ekiti, a majalisar dattawa.

Baturen zabe na jihar, Dr. Tella Adeniran, a wata takarda da ya fitar a Ado-Ekiti, ya ce hukumar ta dakatar da zaben sakamakon rikici da zubda jinin masu kada kuri'a da jami'an hukumar ke fuskanta daga 'yan bangan siyasa.

Adeniran yayi bayanin cewa an fara zaben cike da kwanciyar hankali kafin daga bisani 'yan daba dauke da bindigogi su isa wasu gundumomin yankin tare da fara harbi babu kakkautawa.

KU KARANTA: Bidiyon Amarya mai Adon Fuka-fukai ya Janyo Cece-kuce a Kafar Sada Zumunta

Da duminsa: INEC ta dakatar da zaben maye gurbi na Ekiti saboda zubda jini
Da duminsa: INEC ta dakatar da zaben maye gurbi na Ekiti saboda zubda jini. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fani-Kayode Yasa Masu Tsaron Lafiyarsa sun yi min Tumbur tare da Mugun Duka, Tsohuwar mai Raino

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, a cewar shugaban hukumar zaben, hakan yayin sanadiyar mutuwar masu kada kuri'a uku yayin da dan sanda, mai hidimar kasa da kuma wani jami'in INEC suka jigata.

A wani labari na daban, Dino Melaye, tsohon sanatan da ya wakilci jihar Kogi ta yamma, yace babbar damfarar da ta taba faruwa a Afrika shine yadda aka goyawa Buhari baya ya samu shugabancin kasa a 2015.

Melaye ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a yayin da ya bayyana a wani shiri na gidan talabijin na Channels.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Melaye, wanda yanzu dan babbar jam'iyyar adawa ce ta PDP, ya bar jam'iyyar APC a shekarar 2018.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel