Ku Shirya Birne Nigeria idan Ku Ka Kashe Ortom: Wike Ya Gargaɗi FG
- Gwamnan jihar Rivers Nyesome Wike ya yi martani kan harin da aka kai wa ayarin Gwamna Samuel Ortom
- Wike ya ce a tuhumi gwamnatin tarayya idan aka kashe takwararsa na Benue, Samuel Ortom
- Wike ya kara da cewa muddin aka kashe Ortom za a sake yin wata yakin basasa a Nigeria kuma karshen kasar ya zo
Gwamna Nyesome na Jihar Rivers ya ce a tuhumi gwamnatin tarayya idan aka kashe takwararsa na Benue, Samuel Ortom, Daily Trust ta ruwaito.
An kai wa ayarin motocin Ortom hari a hanyar Makurdi/Gboko a ƙaramar hukumar Makurdi a ranar Asabar.
A martaninsa kan harin, Wike ya ce idan aka kashe Ortom, akwai yiwuwar za a sake yakin basasa a kasar.
KU KARANTA: Matasan Arewa Sun Bawa Sunday Igboho Wa'adin Awa 72 Ya Kwashe Yarbawa Daga Arewa
"Idan ku kashe Ortom, toh ku shirya birne Najeriya, gwamantin tarayya za a tuhuma kuma ta sani cewa Najeriya ta zo karshe kenan," a cewar Wike a Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.
Gwamnan na Rivers ya yi zargin cewa yayin babban zaben 2019, tsohon kwamandan sojoji ta GOC 6 Division a Port Harcourt, Manjo Janar Jamil Sarham da jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar su kammala shirin kashe shi.
KU KARANTA: Buhari Ya Sabunta Naɗin Umaru-Radda a Matsayin Shugaban SMEDAN
A wani labarai na daban, tsohon shugaban majalisar dattawar Nigeria, Dr Bukola Saraki ya roki yan Nigeria su mara wa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin ta samu mulkin kasar a 2023, rahoton Daily Trust.
Saraki ya yi wannan rokon ne yayin da ya ke kaddamar da wasu ayyuka da shirye-shirye da gwamnan tIfeanyi Okowa ya na jihar Delta ya aiwatar a jiharsa inda ya ce har yanzu akwai sauran mutane masu nagarta a PDP.
Ya ce a halin yanzu Nigeria tana cikin mawuyacin hali da suka hada da rashin tsaro da kallubalen tattalin arziki don haka ya bukaci jama'a su sake bawa jam'iyyar PDP wata damar domin su sauya lamuran.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Asali: Legit.ng