Saraki Ya Roki Ƴan Nigeria Su Sake Bawa PDP Dama a 2023
- Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa ya roki yan Nigeria su sake bawa PDP dama a shekarar 2023
- Saraki ya yi wannan kirar ne a yayin da ke kaddamar da wasu ayyuka da gwamman Delta, Ifeanyi Okowa ya yi a Asaba
- Saraki ya ce Nigeria tana fama da wasu kallubale da suka hada da na tsaro da tattalin arziki hakan yasa ya bukaci jama'a su sake bawa PDP dama domin su ga banbanci
Tsohon shugaban majalisar dattawar Nigeria, Dr Bukola Saraki ya roki yan Nigeria su mara wa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin ta samu mulkin kasar a 2023, rahoton Daily Trust.
Saraki ya yi wannan rokon ne yayin da ya ke kaddamar da wasu ayyuka da shirye-shirye da gwamnan Ifeanyi Okowa ya na jihar Delta ya aiwatar a jiharsa inda ya ce har yanzu akwai sauran mutane masu nagarta a PDP.
KU KARANTA: Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta
Ya ce a halin yanzu Nigeria tana cikin mawuyacin hali da suka hada da rashin tsaro da kallubalen tattalin arziki don haka ya bukaci jama'a su sake bawa jam'iyyar PDP wata damar domin su sauya lamuran.
DUBA WANNAN: Da Dumi-Duminsa: Jami'an Ƴan Sanda Sun Kwance Bam a Kano
"Na yi farin cikin kasancewa a wannan wurin domin kaddamar da wannan aikin. Shekaru hudu mun zauna tare a majalisa mun kuma yi aiki tare da kai a lokacin da muka yi dokar Lafiya ta Kasa; Na gamsu da irin ayyukan da ka ke yi a Delta.
"Kasar mu na fama da wasu kallubale a yanzu kuma ina kira ga yan Nigeria su sake bawa jami'iyar PDP wata damar domin su ga banbanci.
"Yadda gwamnatinka ta mayar da hankali wurin gina jiha da kawo cigaba a Asaba, babban birnin jihar abin yabawa ne da jinjina," a cewar Saraki.
Wasu daga cikin ayyukan da ya kaddamar sun hada da ayyukan titi da gyaran gidaje da sauransu.
A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.
Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.
Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng