Matasan Arewa Sun Bawa Sunday Igboho Wa'adin Awa 72 Ya Kwashe Yarbawa Daga Arewa

Matasan Arewa Sun Bawa Sunday Igboho Wa'adin Awa 72 Ya Kwashe Yarbawa Daga Arewa

- Matasan yankin arewa sun bawa Sunday Igbobo wa'addin kwanaki 3 ya kwashe yarbawa daga arewa

- Hakan ya biyo bayan ayyana kafa kasar Yarbawa da Sunday Igboho ya yi a ranar Laraba 19 ga watan Maris

- Matasan arewan sun nemi hadin kan dattawan arewa, masu sarautun gargajiya da hukumomin tsaro wurin korar yarabawa idan wa'addin ya cika

Matasan Arewa sun fadawa mai rajjin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo da ake yi wa lakabi da Sunday Igboho ya kwashe dukkan yarabawa da ke jihohin arewa cikin awanni 72.

Sun yi barazanar cewa za su fattaki dukkan yarabawa da ke yankin Arewa idan wa'addin ya cika ba su fice ba, The Nation ta ruwaito.

Matasan Arewa Sun Bawa Sunday Igboho Wa'adin Awa 72 Ya Kwashe Yarbawa Daga Arewa
Matasan Arewa Sun Bawa Sunday Igboho Wa'adin Awa 72 Ya Kwashe Yarbawa Daga Arewa. Hoto: @Vangaurdngrnews

DUBA WANNAN: Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

Sun kuma nemi taimakon dattawan arewa, masu sarautun gargajiya da jami'an tsaro a yunkurin nasu na koran yarabawa daga jihohin arewa 19 da Abuja.

Sun ce sun dauki matakin ne bayan da Igboho yake ayyana kafa Kasar Yarbawa a ranar Laraba 19 ga watan Maris na 2021.

Matasan, a karkashin kungiyar Arewa Youth Assembly sun kuma bawa Igboho wa'addin awa 72 ya kwashe yarabawa daga arewa idan ba haka ba su kore su da kansu.

Arewa Youth Assembly, ta bakin kakakinta, Mohammed Danlami ta ce Igboho ya dade yana yi wa yan arewa da ke zaune a kudu maso yamma barazana ba tare da wani dalili ba.

KU KARANTA: Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN

Sun ce tunda Igboho na son Yarbawan da ke arewa su fita su tafi su kafa kasar Yarbawa, matasan Arewa za su saukaka masa inda suka nemi ya samar da motocci da za su kwashe mutanensa zuwa kudu maso yamma.

A cewarsu, "Mun bashi wa'addin awa 72 ya fitar da mutanensa idan ba haka ba zamu fitar da su da kan mu.

"Da haka ne muke kira ga dattawan arewa, masu sarautun gargajiya da hukumomin tsaro su taimaka mana wurin fitar da yarbawa daga jihohin arewa 19 da FCT Abuja, domin yinsa cikin lumana ba tare da bawa bata gari dama su tada rikici ba kamar na zanga-zangar Endsars."

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164