Bidiyon Amarya mai Adon Fuka-fukai ya Janyo Cece-kuce a Kafar Sada Zumunta

Bidiyon Amarya mai Adon Fuka-fukai ya Janyo Cece-kuce a Kafar Sada Zumunta

- Bidiyon wata amarya da tayi abinda ba taba yi ba ya janyo maganganu daban-daban a kafar sada zumunta

- Amaryar 'yar arewa da har yanzu ba a san sunanta ba ta bayyana ne sanye da rigar amare ta zamani amma da fuka-fukai

- Wannan shigar ta amaryar ta gigita mutane a kafar sada zumunta saboda ba a taba ganin irin hakan ba

Wata amarya 'yar arewacin Najeriya ta shiga kanun labarai a kafafen sada zumunta bayan bidiyonta na ranar aure ya karade kafar.

Babu shakka 'yan Najerya na kaunar ganin bukukuwa da hotunan ma'aurata, amma kuma suma ma'auratan suna son fito da salon da ba a taba gani ba kuma zai kafa tarihi.

Tabbas wata matashiyar amarya ta cimma burinta kuma babu shakka za a dade ba a manta da salonta ba.

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun sheke 'yan bindiga 2, sun cafke masu siyar da makamai a Kaduna

Bidiyon Amarya mai Adon Fuka-fukai ya Janyo Cece-kuce a Kafar Sada Zumunta
Bidiyon Amarya mai Adon Fuka-fukai ya Janyo Cece-kuce a Kafar Sada Zumunta. Hoto daga @thetattleroom
Source: Instagram

KU KARANTA: Gwamna Masari ya kalubalanci yadda Gumi yake wa 'yan bindiga, yana tafka kuskure

A wani bidiyo da ya yadu, an ga amaryar ta shigo wurin liyafar bikinta cikin shiga ta kasaita da alfarma.

Rigar da ta saka an yi ta ne da atamfa, ta saka kallabi amma kuma wani abu mai kama da fuka-fukai suna makale a bayanta.

Amaryar ta saka fuka-fukan biyu masu kalar zinare tare da wata baza wacce take sanye a karkashin fuka-fukan da kuma jikin rigar.

A natse take tafiya domin tarar da mijinta wanda yake zaune yana jiranta. A yayin da amaryar ta juya, bakin da suka halarta sun sake hangame baki bayan ganin wani kyalle dake biye da ita a baya.

Ga bidiyon amaryar:

Sai dai ganin wannan bidiyon ya saka jama'a da dama suka dinga tsokaci daban-daban. Wasu na yabo, yayin da wasu suka dinga caccakarta.

A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai amfani da @uzomathias a Twitter ya janyo hankalin jama'a inda suka dinga maganganu bayan wani bidiyo da ya wallafa na biki ana bada abinci.

A bayyane, mai raba abincin a bikin ya nuna Garri, kifi, gyada, sikari da kankara a cikin kayan tagomashin da za a baiwa bakin da aka tara.

A wani bidiyo da @uzomathias ya wallafa, an ga mai bada abincin yana zuba garri a kwano inda yake hadawa da sikari, gyada da kankara a sama.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel