Fani-Kayode Yasa Masu Tsaron Lafiyarsa sun yi min Tumbur tare da Mugun Duka, Tsohuwar mai Raino

Fani-Kayode Yasa Masu Tsaron Lafiyarsa sun yi min Tumbur tare da Mugun Duka, Tsohuwar mai Raino

- Anthonia Uchenna tsohuwar mai raino ce a gidan Fani-Kayode wacce tace ya taba sa a yi mata tsirara kuma a zaneta

- Tsohuwar mai rainon tace babu shakka ya saba dukan ma'aikata kuma yana neman ma'aikata mata da lalata

- Ta sanar da yadda ya rike mata albashi na watanni uku da yadda ya neme ta da lalata, lamarin da yasa ta gudu daga gidan

Wata mai raino, Anthonia Uchenna, wacce ta taba aiki a gidan tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ta ce tsohon ministan ya taba umartar masu tsaron lafiyarsa da su yi mata tsirara kuma suka zaneta.

Uchenna, wacce ta ziyarci ofishin Punch, ta sanar da rayuwarta dalla-dalla a gidan.

Ta ce tsohon ministan yayi amfani da 'yan sanda sau babu adadi wurin tsareta.

KU KARANTA: Gwamna Masari ya kalubalanci yadda Gumi yake wa 'yan bindiga, yana tafka kuskure

Fani-Kayode Yasa Masu Tsaron Lafiyarsa sun yi min Tumbur tare da Mugun Duka, Tsohuwar mai Raino
Fani-Kayode Yasa Masu Tsaron Lafiyarsa sun yi min Tumbur tare da Mugun Duka, Tsohuwar mai Raino. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

KU KARANTA: Daga kasashen ketare ake daukar nauyin 'yan bindigan Najeriya, Shugaban NSCDC

Uchennna ta ce: "Fani-Kayode ya umarci masu tsaron lafiyarsa da su yi min tsirara a kan zargin nayi masa sata. Sau da yawa yana kai ma'aikatansa ofishin 'yan sanda inda ake tsaresu na kwanaki.

"Haka nima aka yi min. Fani-Kayode ya umarci wani Bako da yayi min tsirara kuma ya zaneni. Sannan aka kaini ofishin 'yan sanda."

Tsohuwar mai rainon yaran a gidan tsohon ministan ta zargesa da neman yin lalata da ita.

Uchenna ta ce: "Fani-Kayode ya sha nemana da lalata. Wani lokaci ne da matarsa ta umarceni da in kai dan shi dakin shi. Ina kokarin saka yaron a gado ne naji hannun shi a kan mazaunai na.

"Ya yi barazanar dukana idan na ki yadda da shi. Na san cewa yana neman sauran ma'aikata mata da lalata. Na san ya taba lalata da wata Blessing wacce daga baya ta gudu saboda abinda yayi mata."

Uchenna, wacce tace ana biyanta N80,000 a kowanne wata, ta kara da cewa tsohon ministan ya rike mata albashi na watanni uku.

A lokacin da aka tuntubi Fani-Kayode ta waya, yace ba zai yi martani a kan wannan zargin ba.

A wani labari na daban, dakarun Rundunar Operation Thunder Strike sun kashe 'yan bindiga biyu yayin da wasu suka arce da miyagun raunika a samamen da suka kai sansanin 'yan bindigan dake Rafin Rikamba dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

An tattaro cewa wani matukin babbar mota da 'yan bindigan suka sace ya samu tserewa a samamen.

Hakazalika, 'yan sanda sun damke wasu mutum biyu da ake zargi, Abdullahi Samaila da Adamsu Samaila daga karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi dauke da harsasai na siyarwa da suka boye a murfin mota.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng