Tsabar sharri na hada, na mannawa Ortom a 2018, Oshiomhole ya janye zarginsa
- Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole ya karyata kansa a kan zargin da yayi wa Gwamna Samuel Ortom
- A ranar 27 ga watan Yulin 2018 ne Oshiomhole yace Ortom ya handame kudaden jihar, ya hana albashi tare da tabbatar da talauci a Benue
- Tsohon gwamnan yace tsabar karya da sharri ya hadawa Ortom kuma hakan ya taba darajarsa tare da mutuncinsa
Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam'iyyar APC, ya janye zargin da yayi wa Samuel Ortom, gwamnan jihar Binuwai
A wani taron manema labarai na ranar 27 ga watan Yulin 2018, Oshiomhole ya zargi cewa gwamnan yayi waddaka da wasu kudaden Paris Club da na fansa da aka baiwa jihar. Ya zargesa da kin biyan albashi wanda hakan yasa talauci ya tsananta a jihar Binuwai.
Oshiomhole ya yi wannan tsokacin ne yayin da gwamna Ortom ke kokarin sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa ta PDP.
The Cable ta ruwaito cewa, a take Ortom ya bukaci Oshiomhole da ya janye kalamansa kuma ya biya N10 biliyan a matsayin kudin bacin suna.
KU KARANTA: Bidiyon Garri, gyada, sikari da aka raba wurin kayataccen biki sun janyo cece-kuce
KU KARANTA: Daga kasashen ketare ake daukar nauyin 'yan bindigan Najeriya, Shugaban NSCDC
Kusan shekaru uku kenan da lamarin ya faru, Oshiomhole ya aminta da cewa zargin da ya fadi karya ne a kan gwamnan. Ya bayyana hakan ne a wata wallafa da yayi a shafin wata jarida a ranar Alhamis.
"A ranar 27 ga watan Yulin 2018 a hedkwatar APC ta kasa, a matsayina na shugaban jam'iyyar na lokacin, na yi jawabi a kan wasu al'amura da suka faru a jihar Benue.
"A wannan lokacin Gwamna Samuel Ortom na jihar ya sauya sheka zuwa PDP. Na sanar da manema labarai wasu tsokaci da tuni na gano basu tushe balle makama.
"Mai girma Samuel Ortom ya matukar tozarta, an bata masa suna kuma tsokacin bai masa dadi ba.
“A cire siyasa a gefe, Gwamna Samuel Ortom abokina ne kuma dan uwa wanda muke da kamanceceniya mai tarin yawa da shi tare da mutunta juna.
“A matsayinsa na tsohon takwarana kuma wanda waya kadai zan kira ya dauka, duk wani tozarci da zargi da nayi wa Ortom, nayi nadama.
"Saboda alakar da ke tsakaninmu kuma da bukatar wanzuwar zaman lafiya da zumunci, na janye dukkan kalamaina na ranar 27 ga watan Yulin 2018 wanda suka harzuka Ortom.
"A saboda haka, na janye dukkan kalamaina na ranar 27 ga watan Yulin 2018 wadanda suka jihanci Dr Samuel Ortom," Takardar tace.
A wani labari na daban, Aminu Masari, gwamnan jihar Katsina yace baya goyon bayan yadda Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama ke zuwa domin sasantawa da 'yan bindiga.
Gumi yana kan gaba wurin jan hankalin gwamnati a kan ta sasanta da 'yan bindiga duk da yadda suka tsananta wurin kai hare-hare tare da satar 'yan makaranta.
The Cable ta ruwaito yadda Malamin ke kaiwa 'yan bindiga ziyara a inda suke buya cikin dajikan kasar nan domin kokarin kawo sasanci da kuma shawartarsu da su ajiye makamansu.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng