Ba Wanda Ya Canza Maka Kalamanka Kan Kudin Makamai, Gwamna Wike Ga NSA Monguno
- Gwamnan Jihar Rivers ya maida wa NSA martani da cewa babu wanda ya canza mishi kalaman da yayi kan badaƙalar kuɗin makamai
- Gwamanan yace kalaman NSA din gaskiya ne, kuma kuɗin da suka ɓata an ciresu ne daga kuɗin rarar man fetur
- A cewar gwamnan wannan abun kunya ne ga gwamnatin dake ikirarin yaƙi da cin hanci da rashawa
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom, Wike ya fada ma mai bada shawara kan harkar tsaron kasa (NSA), Mejo-janar Babagana Monguno cewa ba wanda ya canza masa magana kan badakalar bacewar kudin makamai.
KARANTA ANAN: 'Yan bindiga sun harbe wani matashi, sun yi awon gaba da Uwa da Ɗanta a Jigawa
Monguno, wanda tun a farko ya janye kalamansa kan cewa ba sawun kuɗin da aka bari wanda akayi amfani da su wajen siyo makamai ga tsofaffin hafsoshin tsaro domin cin galabar yaki da Boko Haram.
Amma gwamna Wike ya ce kalaman nasa gaskiya ne kuma babu bukatar musanta hakan inda ya yi nuni da cewa kuɗin da suka bace an cire su ne daga asusun rarar man fetur, jaridar The Nation ta ruwaito.
A wani jawabi da mai taimaka masa kan lamuran sadarwa Kelvin Ebiri, ya fitar, yace abin kunya ne a ce gwamnatin da ke ikirarin yaki da cin hanci zata bari kudin makamai su yi batan dabo.
Gwamnan ya yi wannan maganar ne lokacin da ya karbi bakuncin shuwagabannin jaridar independent da suka kai mishi ziyara a gidan gwamnati ranar Alhamis.
KARANTA ANAN: 2023: Ku Gaggauta Gyara Kundin Tsarin Zaɓe, PDP Ga Shugaba Buhari Da APC
Yace: "NSA ya fada cewa $1bn da suka daukar mana daga asusun rarar man fetur ba tare da biyan mu kason mu na kashi 13 sun bace. Sun kuma bayyana basu ga makaman ba"
Gwamnan ya kara da cewa:"Amma daga baya NSA ke cewa ba'a fahimce shi dai-dai ba, ina fada muku ba wanda ya canza masa kalamai. Muna sane da cewa babu makaman."
"Shi kan shi shugaban soji yace bai amshi ko sisi ba. To ina kudin suka shiga. Wannan gwamnatin fa dake yaki da cin hanci ce amma yan jarida ba su cewa komai" inji gwamnan.
A wani labarin kuma Tsoho mai shekaru 80 ya koka a kotu kan matarsa mai hana shi jima'i
Wani tsohon malamin jami'a ya koka a gaban kotu kan batun matarsa mai hanashi hakkinsa.
Malamin ya bukaci kotu da ta tilastawa matarsa amincewa dashi a gadon aurensu kasancewar bata yarda
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .
Asali: Legit.ng